Shugaban Rwanda Paula Kagame ya nemi a kawo sauyi a Arsenal

Arsen Wenger Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A karshen kakar bana Arsene Wenger zai bar Arsenal bayan shafe sama da shekara 20

Magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal har yanzu na cigaba da kokawa kan kashin da suka sha a wasan dab da na karshe na gasar cin kofin Turai ta Europa.

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, wanda magoyin bayan Arsenal ne, ya ce rashin nasarar kamar wani mummunan karshe ne ga rayuwar Arsene Wenger a kulob din.

Magoya baya sun yi fatan cewa tawagar za ta kai wasan karshe na gasar sannan ta lashe kofin.

Hakan zai iya ba wa kocin kulob din Arsene Wenger, wanda zai ajiye aiki a karshen kakar bana, damar lashe kofi kafin ya tafi.

Mr Kagame ya wallafa sako a shafinsa na Twitter cewa abin takaici ne halin da Arsenal ta samu kanta a ciki:

"Nawa ra'ayin kan wannan kulob din da na ke kauna - bai kamata a ce irin wannan karshen Wenger ya yi ganin iirn kwarewar da yake da ita da kuma rawar da ya taka a kwallon kafa. Alamu sun dade da bayyana cewa kocin zai tafi ba tare da daukar kofi ba! Har yanzu ina ci gaba da kaunar Arsenal:) Kamata ya yi a daura alhakin batun kan masu kulob din".

Mr Kagame ya kasance daga cikin magoya bayan Arsenal da ke neman a maye gurbin Mr Wenger a kulob din.

Ya kara da cewa yana fatan cewa kulob din zai dawo kan ganiyarsa kamar yadda aka san shi a baya:

"Kamar yadda na fada tun a baya a matsayi na na mai sa ido... akwai bukatar kawo gagarumin sauyi a kulob din. Amma koda wani abu ya sauya, to ba wanda ya dace ba ne. Amma ina fatan alheri ga duk masu ruwa da tsaki a lamarin! Har yanzu muna bukatar Arsenal ta dawo kan ganiyarta kamar yadda aka san ta a baya".

Labarai masu alaka