Ana farautar wani da ya sace kifi a bakin teku a China

Hoton mutumin da ya dora kifin dolphin a kan kafadarsa Hakkin mallakar hoto Miaopai/Btime
Image caption An yada bidiyon da ya nuna mutumin da ke rike da kifin a kafofin sada zumunta

Hukumomi a China na neman wani mutum wanda aka dauki hotonsa lokacin da ya dora wani kifi da ke tashi a cikin ruwa da ake kira Dolphin a kafadarsa a wani bakin teku a yankin Guangdong.

A cewar shafin yada labaru na Btime, an yi amannar cewa mutumin ya tafi da kifin ne zuwa motarsa kafin ya wuce da shi.

Shaidu sun ce an gano kifin ne bayan ya makale a bakin tekun da ke tsibirin Hailing, kuma ya nuna alamun mutuwa.

Jami'ai sun ce mutumin zai iya fuskantar tuhuma idan aka gano shi.

Wata sanarwa da hukumar tsaro ta China ta fitar ta ce ana gudanar da bincike a kan lamarin, kuma ta yi kira ga mutanen da suke da bayani a kan su bayyana a gabanta.

"Kifayen Dolphins na cikin dabbobin da ke samun kariya a China. A kan haka za a hukunta mutumin idan aka gano shi," a cewar sanarwar da hukumar ta fitar.

Shafin yada labarai na Btime ne ya wallafa bidiyon da aka dauka game da lamarin da ya faru a ranar 1 ga watan Mayu wanda daga bisani shafin intanet na Miaopai ya yada, wanda mutane miliyan shida suka kalla.

"Shaidu sun ce sun ga wani kifin ruwa na dolphin wanda ya fara nuna alamun mutuwa a bakin teku," wani jami'in su'ya shaida wa Btime.

"Wani mai yawon bude ido ne ya kama kifin ya dora shi a kan kafadarsa. Daga nan ya zarce a cikin motarsa, da ake kyautata zaton cewa kifin na ciki ."

Mutane da suka rika bayyana ra'ayoyinsu a shafukan sada zumunta na China sun rika sukar mutumin.

"Ban san irin hukuncin da ya kamata a ba mutumin da ya aikata wani abu irin wannan ba," in ji wani da ya bayyana ra'ayinsa a shafin Weibo .

"Idan kana ganin za ka iya, to ka je ka saci kifin ruwa shark mana daga cikin teku, mu ga abin da zai faru. Ya kamata a daina damun kifayen Dolphins," a cewar wani dake amfani da shafin.

Labarai masu alaka