'Ana kwankwadar Kodin a Ghana kamar Najeriya'

Matasa na Shan kodin

Hukumomi a Ghana sun kaddamar da bincike kan wasu shagunan sayar da magani da ake zargi suna sayar da maganin tari mai dauke da kodin ba bisa ka'ida ba.

Jami'an lafiya a kasar na gudanar da bincike akan shaguna 35 a garin Kumasi wadanda ake zargi suna sayar da maganin barkatai.

Binciken kuma ya shafi har da kwayar maganin Tramadol da ke rage radadin ciwo da ake sayarwa ba bisa ka'ida ba a Ghana.

Hukumomin lafiyar na Ghana sun bayyana damuwa kan yadda matasan kasar ke shan ruwan maganin na tari mai dauke da Kodin domin su bugu. Da kuma yadda matasan suke nace ma sa da kuma kwayar Tramadol.

Wannan na zuwa bayan gwamnatin Najeriya ta haramta hada maganin na tari mai Kodin da sayarwa da kuma shigo da shi a kasar.

Najeriya ta dauki matakin ne bayan BBC ta bankado yadda ake sayar da shi barkatai.

Ya kamata sai likitoci sun rubutawa marar lafiya maganin mai dauke da Kodin kafin har a sayar wa da mutum.

Amma BBC ta gano yadda ake hada baki da wasu masu kamfanonin hada magunguna da 'yan kasuwa wurin sayar da shi ba bisa ka'ida ba.

Masu hadawa da sayarwa na bi lungu-lungu da kuma gidajen shakatawa cikin dare domin sayarwa.

Matasa kan hada shi da lemun kwalba ko kuma su sha shi kai-tsaye daga kwalbarsa a wuraren da ake "biki ko gasar shansa".

Alkaluman hukumomi sun bayyana cewa kimanin kwalbar kodin miliyan uku ake sha a kowacce rana a jihohin Kano da Jigawa kawai.

Ana ganin matsalar shaye-shaye wani mummunan al'amari ne da ke rusa rayuwar matasa a Afirka ta Yamma.

Labarai masu alaka