Za a yi zabe a karon farko cikin shekaru tara a Lebanon

Majalisar dokokin sun tsawaita wa'adi har sau biyu Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar dokokin sun tsawaita wa'adi har sau biyu

Al'ummar Lebanon za su zabi sabbin 'yan majalisar dokoki, a karon farko cikin shekaru tara. Zaben na yau ya biyo bayan tsawaita wa'adi har sau biyu da aka yi wa 'yan majalisar da ke ci yanzu.

Za a kada kur'i'un ne a karkashin sabon tsarin zabe, wanda ake fatan zai kai kasar ga samun wakilicin ko wane bangare a gwamnati.

Lebanon dai na fama da bangaranci da rabe-raben siyasa, kuma rikicin da a ke a makwafciyarta Syria ya shafeta inda ta ke fuskantar karuwar bakin haure.

Sai dai masu sharhi sun ce cin hanci da rashawa, bashi da kuma rashin samar da abubuwan more rayuwa na daga cikin manyan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Labarai masu alaka