Yadda Maza ke watsi da hakkin kula da iyali
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yadda Maza ke watsi da hakkin kula da iyali

Wannan matsala ce da ta zama ruwan dare. Yawancin maza suna watsi da nauyin da ya rataya a wuyansu. Ko me ya janyo haka?

Malam Ibrahim bakanike ne da ke samun kudi sosai da za su iya wadatar da matarsa da 'yayansa uku. Amma kuma labarin ya sha bamban da na matarsa saboda a kullum tana fadi-tashi ne domin samun abincin da za ta ci da 'ya'yanta sau uku a rana saboda mijinta kawai yana ba ta kudin abinci ne lokacin da ya ga dama, ko idan ta roke shi.

Haka kuma ba ruwansa da biyan kudin makarantar yara. Kullum sai kukan babu kudi yake yi.

Sai dai kuma a shagonsa, Malam Ibrahim yana ci ya koshi, har da cin tsire da balangu da kayan marmari masu gina jiki.

A kullum yana shiga gida cikinsa a koshe yayin da iyalinsa ke cikin yunwa. Kuma matarsa ba ta damar yin korafi, saboda za a fada ma ta cewa dole ne ta yi hakuri da mijinta.

Wannan matsala ce da ta shafi yanayin zamantakewa a arewacin Najeriya. Matsala ce da ta shafi kowa. Tun daga mazajen da ke wulakanta matansu zuwa ga al'ummar da kullum ke yin kira ga mata su rungumi zaman hakuri.

Shin yaya za a magance wannan matsalar?

Shin ko sai an tanadi tsarin doka domin hukunta wadanda ke wulakanta matansu?

Shin ko matsala ce ta jahilci da ke bukatar wayar da kan al'umma? Shin wane mataki shugabanninmu na gargajiya da addini suke dauka?

Wai me ya sa ake amincewa da mutumin da zai yi watsi da nauyin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na Uba kuma maigida?

Me ya sa a kullum aka fi mayar da hankali ga yin kira ga mace ta kasance mai hakuri?

Labarai masu alaka