Rouhani ya ja kunnen Trump kan Nukiliya

Trump da Rauhani Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Rauhani ya ce Iran ta yi tanadin matakin da ya dace ga duk wata barazana daga Trump.

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi da-na-sanin da ba ta taba yi ba idan har ta yi watsi da yarjejeniyar nukiliya.

Wannan gargadin na Rouhani na zuwa ne a yayin da shugaba Donald Trump ke shirin yanke shawara game da janye wa daga yarjejeniyar a ranar 12 ga Mayu.

Mista Trump ya dade yana sukar yarjejeniyar, wacce manyan kasashen duniya shida hadi da Amurka suka kulla da Iran kan nukiliya.

A 2015 Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da China da kuma Jamus suka amince su cire wa Iran takunkumi da nufin takaita shirinta na nukuliya.

Iran dai ta dade tana jaddada cewa shirinta na bunkasa makamashi ne ba na makamin nukiliya ba, kamar yadda kasashen na duniya ke tunani.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi ga Trump kada ya janye daga yarjejeniyar.

Amma duk da haka Mista Trump ya yi barazanar cewa Amurka za ta janye daga Yarjejeniyar a ranar 12 ga Mayu, wato karshen wa'adin kwanaki 120 da ya diba domin nazarin yarjejeniyar.

A nasa bangaren shugaban Iran Hassan Rouhani ya ce muddin Amurka ta janye, to za ta yi da-na-sanin da ba ta taba yi ba a tarihin kasar.

Rouhani ya ce: "Iran ta yi tanadin matakin da ya kamata ta dauka da za ta tunkari duk wata barazana daga Trump."

Amurka ta amince da yarjejeniyar ne a zamanin tsohon shugaba Barack Obama.