Ingila: An zabi 'yar shekara 19 a matsayin kansila

Ellie Emberson Hakkin mallakar hoto Ellie Emberson
Image caption Ellie Emberson ta shafe watanni shida tana yakin neman zabe kafin aka zabe ta

Ellie Emberson, mai shekara 19 na cikin matasa masu karancin shekaru da aka taba zaba kansila a Ingila, bayan zaben kananan hukumomi da aka gudanar ranar Alhamis.

Ta lashe kujerar kansila ta karamar hukumar Reading a karkashin jam'iyyar Labour a gundumar Minster.

Za ta rike mukamin na shekaru hudu masu zuwa.

Zaben nata zai kawo wani sauyi a siyasar yankin, domin yawancin kansilolin da ake zaba su kan haura shekaru 60 da haihuwa.

Ta ce tana fatan wakiltar matasan yankin da a shekarun baya ba a jin duriyarsu a siyasance.

"Matasa na bukatar wakilci. Akwai matasa a wannan gundumar, saboda haka akwai bukatar wani ya basu wakilci domin a san irin bukatunsu."

"Shi yasa na ce bari in gwada da kaina."

Ellie Emberson ta ce tana fatan samun goyon bayan karamar hukumar wajen samar da wasu shirye-shirye da zasu taimakawa matasa, kuma za tayi aiki da jam'iyyarta ta Labour domin cimma burinta na samar da gidaje ga matasan yankin.

An zabi wasu kansilolin masu kananan shekaru

Image caption An zabi masu shekaru 18 har su biyu, Jake Cooper (hagu) da Joe Roberts wadanda suka lashe zabukansu a Dudley a karkashin jam'iyyar Conservative

A zabukan da aka gudanar a yankin Dudley, an zabi Jake Cooper, mai shekara 18 a mazabar Belle Vale.

Shi kuma Joe Roberts, wanda shi ma mai shekara 18 ne, ya lashe zaben gundumar Halesowen North.

Labarai masu alaka