An rantsar da Putin a wa'adi na hudu

An rantsar da Vladimir Putin a wani sabon wa'adi na hudu na shugabancin Rasha bayan nasarar da ya yi a zaben watan Maris.

Hakkin mallakar hoto AFP

Baki dubu biyar ne suka halarci bikin rantsar da shi da aka yi a kasaitaccen dakin taro na Kremlin inda ak rantsar da shi.

Shugaban zai tsawaita shekara 18 da ya shafe yana mulkin kasar, wanda magoya bayansa ke cewa ya farfado da martabar kasar a duniya, yayin da 'yan hamayya ke bayyana mulkinsa da ta kama karya.

A ranar Asabar da ta gabata, aka samu yamutsi tsakanin masu zanga-zangar adawa da salon mulkin shugaban da jami'an tsaro

Sama da Mutum dubu daya aka cafke a biranen kasar 19 lokacin zanga-zangar.

Putin zai karbi rantsuwar kama aiki ne a dandalin da aka nada tsofaffin sarakunan Rasha, a kasar da ta fi kowacce fadin kasa a duniya, kuma za a takaita shagulgula.

Rahotanni sun ce wadanda suka ba da gudunmawa a lokacin yakin neman zaben Mista Putin, mai shekaru 65, ne kawai za su halarci bikin rantsar da shi.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Vladmir Putin na fuskantar adawa daga ciki da wajen kasar

Mista Putin na fuskantar manyan kalubale da kuma takukuman karayar tattalin arziki da tasirinsu ke bayyane.

Rasha na ci gaba da fuskantar rikicin diflomasiya da kasashen yamma a kan kasar Ukraine da Syria da kuma zargin da ake ma ta na kutse a harkokin zaben kasashen ketare.

Labarai masu alaka