Ba kodin ne kawai ke haukatar da matasa ba - Ganduje
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ba kodin ne kawai ke haukatar da matasa ba - Ganduje

Gwamnan jihar Kano ya ce dole sai hukumomi sun kara kaimi domin shawo kan matsalar shan miyagun kwayoyi da ta addabi kasar musamman a jiharsa.

Abdullahi Umar Ganduje ya ce akwai kwayoyi da dama da suke yi wa matasa illa baya ga kodin.

"Akwai kwayoyi da dama da ake sayarwa ba bisa ka'ida ba, wadanda ke da illa sosai," a cewar Ganduje, sai dai bai yi karin haske kan wadannan kwayoyi ba.

Gwamnan na mayar da martani ne ga rahoton BBC wanda ya bankado yadda shan kodin ke haukatar da matasa a Najeriya musamman a arewacin kasar.

Rahoton ya kuma tona aisirin wadansu masu kamfanonin hada magunguna da kuma dillalai wadanda ke hada baki wurin sayar da magungunan ba bisa ka'ida ba.

Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce "Akwai manya-manyan matakai wadanda dole ne sai an daukesu musamman wajan shigo da wasu kwayoyin da ba a yi su a kan nagartar da aka shirya a yi su ba."

Ya kuma ce gwamnatinsa na daukar mataki a kan matsalar.

"A yanzu dai haka muna da kwamiti na kar-ta-kwana wanda yake bincikar masu sayar da magunguna, suna zuwa suto-suto dinsu kuma suna tare motoci a hanya".

Bayanai sun nuna cewa akalla kwalaban kodin miliyan uku ne ake sha a kullum a jihohin Kano da Jigawa kawai.

Tuni dai gwamnatin kasar ta haramta shigowa da kuma sarrafa maganin tari mai dauke da kodin a kasar.

Maganin Kodin - yadda girman matsalar ta ke

  • Kodin magani ne da ke rage zafin ciwo ko na jiki amma yana cikin magungunan da ke sa maye.
  • Idan aka sha shi fiye da kima, to yana janyo tabin hankali kuma yana yin illa ga koda ko hanta ko zuciyar mutum
  • An fi hada maganin tari na kodin da lemun kwalba kuma dalibai ne suka fi shansa.
  • Daga kasashen waje ne ake shigowa da kodin, amma a cikin Na jeriya ne kamfanoni fiye da 20 suke hada magani
  • Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar na kokarin kawarda da matsalar.
  • A samamen da taka kai a baya-baya nan, ta kwato kwalaben Kodin 24,000 daga cikin wata babbar mota a jihar Katsina.
  • Ta'ammali da kodin babbar matsala ce a Afirka, inda ake samun rahotanni game da wadanda ba su iya rabuwa da shi a Kenya da Ghana da Niger da kuma Chadi
  • A shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta hana amfani da shi a kasar sakamakon rahoton da ta samu game da yawan masu ta'ammali da shi a matsayin kayan maye

Labarai masu alaka