'Yan shi'a sun yi zanga-zanga a gidan Tinubu a Legas

'Yan Shi'a a Lagas

Kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta Shi'a (IMN) ta bukaci Senata Bola Ahmed Tinubu ya sa baki domin sakin jagoranta Sheikh Ibrahim El-Zakzaky.

Gamman magoya bayan kungiyar ne suka gudanar da zanga-zanga a Legas da ke kudancin Najeriya a yau Laraba.

Sun yi tattaki har zuwa gidan tsohon gwamnan jihar Bola Ahmed Tinubu kuma jagoran jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Wakilin BBC ya ce 'Yan Shi'ar sun gabatar da wata takardar koke ga Tinubu zuwa ga shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

Sannan sun bukaci jagoran na APC ya sa baki domin a saki shugabansu El Zakzaky.

Wannan na zuwa bayan wani gargadi da tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya yi game da ci gaba da tsare jagoran na 'yan Shi'a a Najeriya.

Mista Campbell ya ce idan har Najeriya ta ci gaba da tsare El Zakzaky, za a iya samun rikici irin na Boko Haram.

Magoya bayan Sheikh Zakzaky sun dade suna zanga-zanga cikin lumana domin neman a sako mu su jagoransu.

A ranar 12 ga watan Disamban 2015 ne 'yan shi'ar suka yi arangama da sojoji a garin Zaria da ke jihar Kaduna, lamarin da ya kai ga rasa daruruwan rayuka.

Gwamnatin jihar Kaduna ta haramta kungiyar tare da hana ta gudanar da taruka, bayan ta tuhume Zakzaky da wasu mabiyansa da laifuka takwas ciki da har laifin kisa.

Sai dai kungiyar ta sha musanta zargin.

Labarai masu alaka