Iran da Isra'ila na barin wuta a Syria

Yadda aka harba makaman roka a tuddan Golan
Image caption Yadda aka harba makaman roka a tuddan Golan

Isra'ila ta ce ta lalata kusan dukkan kayayyakin yaki na sojin Iran a Syria a matsayin martani ga Iran din sakamakon hare-hare da ta kai mata da makaman roka a Tuddan Golan.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce Iran ta harba wa dakarunta makaman roka 20 a cikin dare a wuraren da suke zaune.

A matsayin martani kuma, Isra'ilar ta kai hari wuraren da Iran ta boye makamanta da kuma cibiyoyin leken asirinta.

Babu wani martani daga Iran, wacce matakinta na tura dakaru Syria domin su taimaka wa Shugaba Bashar al-Assad ya tayar da hankalin Isra'ila.

Kafar yada labaran Syria, ta rawaito cewa sojojin saman kasar sun mayar wa Isra'ila martani a kan iyakarta da kasar inda ta harbo makamanta masu linzami.

To sai dai kuma wata majiya daga dakarun ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Sana cewa an harba wasu makaman kan wata bataliyar sojin saman kasar da kuma wajen ajiye makamai.

Isra'ila dai ta sha alwashin kawo karshen abinda ta dauka fadada ikon da Iran ke yi a Syria, sannan kuma ta yi amanna cewa ta kai hare-hare ta sama kan abubuwa masu muhimmanci ga Iran.

Ciki kuwa har da harin da aka kai kan sansanin sojin ta na sama a watan Afrilu wanda ya yi sanadin rasa rayukan dakarun Iran na musamman bakwai.

Me yasa Isra'ila ke kai hari kan muradun Iran?

Iran ita ce babbar abokiyar gabar Isra'ila, kuma ta sha kira da a kawar da kasar a doron kasa.

Kazalika babbar abokiyar shugaban kasar Syria ce, kuma ta tura daruruwan dakarunta zuwa kasar. inda ta ce ta tura dakarunta a matsayin masu bawa dakarun Syria shawara ne.

Dubban mayakan sa kan da suka samu horo daga Iran, suma na yaki tare da dakarun Syria.

Yayin da Iran ke goyon bayan shugaban Assad, ta kara yawan dakarunta a Syria, abinda Isra'ila ke dauka a matsayin babbar barazana.

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya sha gargadin cewa Isra'ila za ta yaki Iran koba ba dade ko ba jima domin ta kawo karshen hare-haren da ake kai mata.

Labarai masu alaka