Wasu jiga-jigan APC sun gargadi Buhari da kuma jam'iyyar

APC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jam'iyyar APC na fama da rigingimu kala-kala a daidai lokacin da ake fuskantar zaben 2019

Wasu jigajigai a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya sun yi Allah-wadai da yadda ake tafiyar da jam'iyyar da kuma gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

Manyan 'yan siyasar wadanda suka koma jam'iyyar daga sabuwar PDP sun ce ba a "damawa da su a harkokinta da kuma gwamnati, sannan ana nuna musu wariya da kokarin dakile su" ta kowacce hanya.

Wadannan kalaman na kunshe ne a wata wasika ta suka aika wa shugaban jam'iyyar da kuma Shugaba Buhari, wadda Alhaji Kawu Baraje da Olagunsoye Oyinlola suka sa wa hannu a ranar 17 ga Afrilu, inda suka ce ya kamata a ji kukansu idan har ana son yin nasara a zaben 2019.

'Yan siyasar, wadanda Alhaji Kawu Baraje ya jagoranci tawagarsu zuwa ofishin Shugaban jam'iyyar na kasa John Oyegun, sun ce sun bai wa jam'iyyar da gwamnatinta mako guda domin a biya musu bukatunsu.

Wannan korafi na zuwa ne a daidai lokacin da jam'iyyar ke zaben shugabanninta a matakai daban daban, zaben da tuni ya fara haifar da rikici da rabuwar kawuna a jam'iyyar.

Cikin wadanda suka koma APC daga sabuwar PDP a 2014 akwai tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da na Sokoto, Aliyu Wamako, da na Rivers, Rotimi Amaechi, da na Gombe, Danjuma Goje, da na Kwara Bukola Saraki.

Sai dai babu tabbas ko suna goyon bayan wannan takardar korafi da aka gabatar a yanzu domin babu sa hannunsu a kai kuma ba su ce uffan ba kawo yanzu.

Har wa yau 'yan siyasar sun hada da tsohon gwamnan Kebbi, Adamu Aliero, da kuma na Adamawa, Murtala Nyako.

Wasikar ta ce 'yan siyasar suna neman karfafa jam'iyyar gabanin zaben 2019, amma Shugaba Buhari bai nuna ya san da gagarumar gudummar da suka bayar wajen nasarar jam'iyyar a zaben 2015 ba.

Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption Sanata Aliyu Wamako na cikin 'yan PDP da suka koma APC a 2014

'Yan sabuwar PDP din sun ce an nuna musu wariya wajen nada 'yan majalisar zartarwa, inda aka nada tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, duka da cewa jiharsa ba ta bayar da wata gudammawar kuri'u na azo a gani ba a zaben.

Sun kara da cewa anki a ba su mukamai yayin da gwamnatin APC ta ci gaba da bai wa tsaffin 'yan jam'iyyar CPC da ACN da ANPP da APGA da kuma wadanda ma ba su da jam'iyya mukamai.

Wasikar kuma ta ce a lokacin da 'yan sabuwar PDP suka yi takarar shugabancin majalisar dattijai da na wakilan Najeriya, an ci zarafinsu kamar su ba 'yan jam'iyyar APC ba ne.

Kwanakin baya ne jam'iyyar adawa ta PDP ta kafa kwamiti domin zawarcin tsaffin 'ya'yanta da suka dawo karkashin Tsohon Gwamnan Cross River, Liyel Imoke.

Shi kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya bai wa tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu, aikin sasanta tsakanin 'yan jam'iyyar ta APC.

Labarai masu alaka