Kun san shugaba mafi tsufa a duniya?

Tsohon fira ministan Malaysia kuma dan takarar 'yan hammaya da ya yi nasara a zabe Mahathir Mohamad lokacinda yake magana da 'yan jarida a Kuala Lumpur a ranar 10 ga watan Mayu , 2018 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mr Mahathir mutum ne mai son yin barkwanci

Mahathir Mohamad mai shekara 92 na daf da zama zababben shugaban kasa mafi tsufa a duniya.

An san shi da fadin gaskiya komi dacin ta kuma Mista Mahathir a cikin natsuwa yake magana a kan shekarunsa.

"Eh har yanzu ina raye," kamar yadda ya fada wa taron manema labarai bayan nasarar da ya samu a zaben Malaysia.

Mutane da dama suna nuna damuwa akan lafiyarsa da ake ganin zai zama sabon shugaban kasar Malaysia da kuma ko gagaggen dan siyasar zai iya tabuka wani abin a zo gani.

A watan Maris ya bayyana a wata tattaunawar da ba a gayyace shi ba, inda ake magana a kan ko ya tsufa ya rike mukamin firaminista.

Ya sanar da isowarsa a shafin Twitter yana cewa: " Gani nan na iso, ku yi maganarku a gabana."

"Rukunin shekaru guda biyu ne ake da su. Na farko shi ne idan ka manyanta saboda shekarunka yayin da dayan na da nasaba ne da yanayin jikin mutum," kamar yadda ya fadawa taron jama'a.

"Ta fuskar kiwon lafiya a gani na har yanzu kwalkwalwata garau ta ke." a cewarsa.

Sai dai kafofin watsa labarai sun bayyana Mahathir Mohammed a matsayin tsoho mai kazar-kazar kuma duk da cewa babu alamun tsufa sosai a jikinsa amma ya yi fama da rashin lafiya da ya shafi har da bugun zuciya sau biyu.

Ba ya boye-boye game da mutuwa.

"Idan zuciyata ta daina buguwa to na mutu ke nan," haka ya bayyana a jawabin da ya yi da aka watsa kai-tsaye a shafin Facebook a bara.

"Shekarata 91 kuma nan bada jimawa ba zan cika 92. A kan haka ya kamata mu dubi hanyoyin da ba za su rika kawo muna damuwa ba a zuciyarmu."

'Ba ni da isasshen lokaci'

Mista Mahathir, wanda ya yi fiye da shekara ashirin yana rike da mukamin Firaminista kafin ya sauka daga mulki a shekarar 2003, ya ba kowa mamaki lokacin da ya sake komowa fagen siyasa a bara

Ya jingine ritaya da ya yi kuma ya sauya sheka zuwa jam'iyyar 'yan hamayya domin kalubalantar Najib Razak wanda a baya yaronsa ne.

"Idan na ce ina son na yi barci kuma na yi ritaya tare da jiran lokacin da zan koma ga mahalacina, ina ganin akwai son kai a ciki," inji Mista Mahathir a wata hirar da ya yi a shekarar 2017.

A cikin shekarun da suka gabata yawan masu goyon bayan Mista Mahathir ya karu. Sai dai kuma yana da masu sukarsa da dama.

Sai dai dan siyasar bai damu sosai ba a kan yadda duniya za ta tuna shi ba.

"Ban damu ba akan ko mutane za su tuna da ni ko kuma aa," in ji Mista Mahathir a wata hira da aka yi da shi.

"Idan mutane sun tuna da ni , to sun kyauta amma idan ba su tuna da ni ba, wannan ba wani abu ba ne domin na riga na mutu."

Labarai masu alaka