Makiya na neman ganin bayan Buhari - Adesina

Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fadar Shugaban kasa ta ce ranar Asabar Shugaba Buhari zai koma gida

Fadar shugaban Najeriya ta yi zargin cewa makiya na kokarin bata sunan Shugaba Muhammadu Buhari domin ganin ya fadi a zaben 2019.

Mai magana da yawun shugaban Femi Adesina, ya ce wasu mutane na sauya ma'anar kalaman shugaban da jirkita su domin cimma manufar siyasa.

Mr Adesina na mayar da martani ne kan korafe-korafen da ake yi ne kan jinyar da shugaban ke zuwa Ingila.

A ranar Talata ne Shugaba Buhari, mai shekara 74, ya sake komawa Ingila domin ganin likitocinsa - wannan ne karo na hudu da shugaban ke tafiya jinya Landan.

A watan Agustan bara ne ya koma kasar bayan shafe wata uku yana jinya a Ingila.

'Yan kasar da dama dai na cigaba da sukar wannan matakin, suna masu cewa kamata ya yi shugaban ya mayar da hankali wurin gyara fannin lafiya na kasar.

Wasu sun bayar da misalin wasu kalamai da aka ce Shugaba Buhari ya yi a baya, inda ya soki yadda ake tafiya ganin likita a kasashen waje, amma sai ga shi shi ma ya zo yana yin hakan.

Sai dai Femi Adesina ya ce ana sauya wa kamalan shugaban ma'ana ne.

"Da farko suna mayar da hankali ne wurin sauya wa kalamansa ma'ana, amma da suka ga hakan ba ya tasiri,... a yanzu sun koma kirkirar karya da hanyar amfani da shafukan sada zumunta," a cewarsa.

Adesina ya bayar da misali ga jawabin da Buhari ya yi a shekarar 2015 lokacin yana dan takara a Chatham House, a Landan, inda ya ce "an sauya" wasu kalmomi daga cikin jawabin domin nuna cewa shugaban ya ce "bai ga dalilin fita waje neman magani ba bayan akwai likitoci a Najeriya".

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ku kalli bidiyon gidan da Buhari yake jinya a London

Ya kara da cewa amma Allah ya sa cikakken jawabin da shugaban ya yi na nan a bayyane kamar yadda aka wallafa a wancan lokacin.

Wannan batu na rashin lafiyar Shugaba Buhari ya dade yana haifar da ce-ce-ku-ce a kasar, musamman ganin cewa ya tafi Landan din ne a lokacin da ma'aikatan lafiya a kasar ke yajin aiki.

Ma'aikatan na zargin gwamnati da kasa biya musu bukatunsu da suka hada da inganta harkokin lafiya a kasar ta hanyar samar da kayan aiki. Sai dai gwamnatin ta ce tana iya kokarinta.

A kwanan baya ne Shugaba Buhari ya sanar da aniyarsa ta neman wa'adi na biyu a zaben kasar da za a yi a badi.

Sai dai wasu na kara nuna shakku kan koshin lafiyarsa musamman bayan da ya sake tafiya Landan ganin likita.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin mako guda da zai ga likita bayan da ya gana da likitocin nasa a kan hanyarsa ta dawowa daga Amurka a makon da ya gabata.


Bayani kan rayuwar Shugaba Buhari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce rashin lafiyar da ya yi a farkon bara ta tsananta sosai
  • Shekararsa 72
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa.