Zanga-zangar matasa kan yawan kisan mutane a Zamfara

Zanga-zangar matasan Zamfara Hakkin mallakar hoto Save Zamfara Group

Matasa a jihar Zamfara a arewacin Najeriya sun gudanar da zanga-zanga domin nuna damuwa da yawaitar kisan rayuka da ake yi a jihar.

Matasan sun gudanar da zanga-zangar Lumana ne a Gusau babban birnin Jihar a yau Alhamis karkashin inuwar Kungiyar Save Zamfara Group.

Kuma sun ce sun yi hakan ne domin janyo hankalin mahukuntan jihar ga irin hasarar rayukan da ake yi a kullum.

Matasan sun yi tattaki zuwa gidan gwamnatin jihar da majalisa da kuma fadar mai martaba Sarkin Gusau.

Sai dai matasan ba su samu haduwa da gwamnan jihar ba amma sun gana da shugabannin majalisa.

Muhammad Abubakar Gumi mataimakin shugaban majalisar jihar da ya saurari koken matasan ya ce gwamnati na iya kokarinta domin magance matsalar.

Ya shaida wa matasan cewa majalisa ta ji kokensu tare yin alkawalin za su dauki matakan da suka dace.

Bashir Maru wanda ya jagoranci gangamin matasan ya ce sun fito ne domin su yi Allah-Wadai da abin da ke faruwa a jiharsu da nuna rashin jin dadi ga matakan da gwamnati ke dauka tare da kuma jajantawa wadanda masifar ta shafa.

Ya ce a kullum akan ji labarin kashe-kashen da ake yi a jihar ne kawai idan an kashe rayuka da yawa a lokaci guda, amma kuma duk ranar Allah sai wani dan jihar ya rasa ransa a hannun 'yan bindiga.

Hakkin mallakar hoto Save Zamfara Group
Image caption Majalisar jihar Zamfara ta bukaci Matasan su gabatar da kokensu ga Majalisar Tarayya.

An dade ana fama da kashe-kashen mutane a jihar Zamfara, al'amarin da ya addabi mazauna yankin.

A kullum dai gwamnatin jihar da ta Tarayyana na cewa suna iya kokarinsu domin kawo karshen kashe-kashen.

Sai dai duk da kokarin da hukumomi ke cewa suna yi har yanzu ba a samu saukin masifar ba.

Labarai masu alaka