Trump ya sanar da kasar da zai gana da Kim Jong-un

Kim Jong-un and Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai gana da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong-un a kasar Singapore a ranar 12 ga watan Yuni.

"Ganawar za ta kasance ta musamman ga zaman lafiya a duniya" kamar yadda shugaban na Amurka ya wallafa a shafinsa na twitter.

A watan Maris ne Mista Trump ya amince zai gana da Mista Kim, a wani mataki da ya zo wa duniya da mamaki.

Shugabannin biyu sun dade suna musayar zafafan kalamai tare da yi wa juna barazanar yaki.

Wannan ci gaban na zuwa bayan wata tattaunawa da aka yi mai cike da tarihi tsakanin Koriya ta Arewa da kuma Koriya ta Kudu.

Kuma sanarwar Trump na zuwa ne bayan ya tarbi wasu Amurkawa guda uku da Koriya ta Arewa ta saka.

Koriya ta Arewa ta saki Amurkawan ne a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo yake ziyara a Pyongyang.

Babu dai wani shugaban Amurka da ya taba ganawa da shugaban Koriya ta Arewa.

Fadar White House ta ce sakin Amurkawan wata alama ce ta samun nasara gabanin ganawar Trump da Jong-un.

Trump ya ce wannan wata babbar dama ce ta aiwatar da wani abu muhimmi.

Batun nukiliyar Koriya ta Arewa ne dai muhimmin batun da zai mamaye ganawar, bukatar da Amurka ta dade tana neman gwamnatin Koriya ta arewa ta jingine.

Kasar ta gudanar da gwajin nukiliya sau shida duk da Allah-wadai da takunkumin manyan kasashen duniya.

Zuwa yanzu dai babu wani bayani da ya fito daga bangaren Koriya ta Arewa game da tattaunawar, musamman kan bukatunta ga Amurka.

Ana ganin Koriya ta Arewa za ta nemi janye dakarun Amurka 30,000 daga Koriya ta Kudu.