Yara 400,000 na fuskantar yunwa a Congo

Yunwa na hallaka mutane musamman yara a Congo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yunwa na hallaka mutane musamman yara a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa yara dubu dari hudu ne a yankin Kasai da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ke fama da matsanancin karancin abinci mai gina jiki.

Majalisar ta ce kananan yaran na matukar bukatar dauki na gaggawa domin ceto rayukansu.

Hakan na kunshe ne cikin wani rahoto da Asusun Asusun kula da kananan yara na Majalisar wato UNICEF ya fitar.

Rahoton ya bukaci a samar da karin kudaden da za a yi amfani da su wajen kara yawan cibiyoyin samar da abinci mai gina jiki ga yaran da ke fama da yunwa.

Yankin wanda a baya ya kasance daya daga cikin wadanda aka fi zaman lafiya a kasar ta Congo ya tsunduma cikin rikici ne a shekara ta 2016, abinda ya kori dubban al'umma daga muhallansu.

Wasu da suka tsere na komawa yankunan da suka bari, sai dai ba a yi noma ba, saboda haka abinci ya yi karanci.

Wadanda suka fi shan wahala su ne yara kanana:

UNICEF ya yi kiyasin cewa kusan yara 800,000 na fama da karancin abinci mai gina jiki.

Haka kuma Asusun ya ce matukar babu wani tallafi na kusa-kusa, akwai yiwuwar cewa za su mutu.

UNICEF ya kuma bukaci a taimaka da tallafin kudi har dala miliyan 88 domin aikin agaji a yankin Kasai.

Labarai masu alaka