Kalli wasu abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Wasu daga cikin hotuna mafi kyau da aka dauka a wasu kasashen Afirka a karshen mako

Image caption A ranar Juma'a ne dubban mutane suka taru a unguwar Goron Dutse domin halartar jana'izar shugaban darikar Tijjaniya a Najeriya Khalifa Isyaka Rabi'u, a Kano.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mutane a Libya sun yi shigar gargajiya a faretin sojoji da aka yi a gabashin Benghazi.
Image caption Sahun Sallar Jana'izar Marigayi Isyaka Rabiu a masallacin gidansa
Hakkin mallakar hoto Zaidu Bala facebook
Image caption Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje na cikin mutanen da suka tarbi gawar marigayin yayin da ta iso Kano.
Hakkin mallakar hoto Aisha Buhari Twitter
Image caption Matar shugaban kasar Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya ga iyalan marigayin a ranar Juma'a a Kano.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mai tallan kayan kawa ta saka tufafin da Yemi Shoyemi ya dinka a makon tallata kayan kawa na amare da aka yi a birnin Lagos na Najeriya
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A nan kuma wani Ango ne yake rawa a ranar daurin aurensa a birnin Lagos na Najeriya.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wadannan matan sun sha ado da kwaLliya a wajen bikin daurin aure A lAGOS
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A birnin kasuwanci na Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu, an yi bajekolin wasu hotunan da suka nuna yadda aka rika fuskantar wariyar launin fata da aka kawo karshesa a shekarar 1994.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani zane da aka gano a kabarin Janar Iwrya a makabartar Saqqara da ke Masar. Iwrhya soja ne a lokacin mulkin Fir'auna Seti na I da firauna Ramesses na II.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu masu raye-raye daga Rasha na rawa a wurin yawon bude ido na Suez...
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Julia Anderson 'yar Birtaniya ce da ke rawar Larabawa kuma ana samun karuwa a yawan 'yan kasashen waje da ke rawar Larabawa da ake kira Belly dancing a Masar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Idan muka koma garin Cape Town na kasar Afrika ta Kudu, wani mutum na shan tabar wiwi a zanga-zangar neman halatta shan tabar.

Labarai masu alaka

Labaran BBC