Yadda wani mata-maza ya kusa kashe kansa saboda takaici a Kano

Halima Umar Sale na tattaunawa da Misbahu (ba asalin sunan shi ba ke nan)
Image caption Mai yiwuwa tsangwama da kyara ne kan sanya mata-maza su boye halin da suke ciki

Tun lokacin da ya fara wayo, Misbahu (ba sunansa na asali ba ke nan) ya fahimci cewa halittarsa ta sha bamban da ta sauran yara.

Tun a lokacin ne kuma yakan shiga damuwa ya koma gefe ya yi ta kuka.

Sai dai kamar yadda za a karanta a wannan rahoto na musamman da Halima Umar Saleh ta rubuta, ashe kukan targade yake yi, karaya na nan tafe.

A duk lokacin da aka samu karuwa ta haihuwa akan yi murna da farin ciki. Amma Umma da Tunau (ba sunansu na asali ba ke nan) murnar su ta koma ciki lokacin da suka fahimci cewa jaritin da suka haifa na da al'aurar maza da ta mata. Matsalar ita ce: namiji aka haifa ko mace? Ba su tabbatar ba.

"Lokacin da aka haifi yaron nan — shekara 24 da suka gabata — na shiga damuwa kwarai da gaske", inji Tunau.

Da Tunau da maidakinsa suka garzaya asibiti don a warware musu zare da abawa, sai likitoci suka ce ba za a iya komai a kan wannan lamari ba sai yaron/yarinyar ya/ta yi kwari.

Don haka suka dawo gida jikinsu a sanyaye.

"Ba don zuciya irin ta Musulunci ba, da na hallaka kaina don na daina ganin wannan abun bakin ciki.

"Daga baya da na yi tunani na ga duk yadda Allah Mahalicci ya so haka zai yi a kan mutum, sai kawai na fawwala masa lamarin na dauki dangana", a cewar Tunau.

Bayan tuntubar limamin kauyensu da wan Tunau, ma'auratan sun yanke shawara su sanya wa jaririn suna Misbahu.

Mai yiwuwa wannan shawara ta mahaifansa ta yi tasiri wajen zabin jinsin da Misbahu zai so ya karkata a gaba, amma ya ce tasowar da ya yi yana komai a cikin maza ita ta ja hankalinsa.

Galibi dai wanda bai san su ba, ba zai gane mata-maza da ganin su ba, har sai sun fara girma. Sai dai duk da haka Misbahu ya sha shiga wani irin hali idan ya dubu halitarsa ya ga ta yi daban da ta sauran yara 'yan uwansa.

"Gaskiya na shiga tashin hankali sosai saboda yadda na tsinci kaina…sai dai in koma waje daya in yi ta kuka", inji shi.

Amma fa wannan tashin hankalin nafila ne idan aka kwatanta da wanda ya shiga lokacin da ya fara girma kuma, kamar ko wata 'yar budurwa, ya fara kirgen dangi—ma'ana, nono ya fara bayyana a kirjinsa—sannan ya fara al'ada.

"Wallahi na shiga damuwa lokacin da na fara al'ada, ta kai ta kawo duk wata idan zan yi al'ada sai na yi ta fama da ciwon ciki mai tsanani," inji Musbahu.

Tsangwama da kyara

A wasu sassa na duniya, masu halittar da ba a saba ganin irinta ba kan fuskanci tsangwama da kyara.

Image caption Tsangwama kan sanya mutane su shiga mummunan hali, inji Dokta Bulus Yaksat

Shi ma Musbahu ya fuskanci irin wannan tsangwama daga wajen mutane musamman ma abokansa.

"Da yawa akwai wadanda muke mu'amala da su, ko da ba na gun sai sun yi da ni, ko kuma ina zuwa gurin wasu za su kama yi min dariya.... Ko na bar gun wasu abokan arzikina za su gaya min", inji Misbahu.

Daga karshe dai wannan tsangwama da kyara suka hana shi ci gaba da karatu.

"A da ina zuwa makaranta amma ganin yadda ake yawan tsokanata ko na je ba na mayar da hankali kan karatun, sai kawai na daina zuwa makarantar.

'Na kusa kashe kaina'

Sakamakon wannan hali na kunci da ya shiga, sai da Misbahu ya yi tunanin kashe kansa: "Akwai lokacin da na yi tunanin da ma ban zo ba, ko kuma in kar kaina....

"Akwai lokacin da na so in [kashe kaina] kawai [abin da ya hana ni shi ne] na gaya wa mahaifiyata [sai] ta ce in yi hakuri, duk abin da Allah Ya yi, komai ya yi farko zai yi karshe".

Wannan na cikin hadurran da tsangwama da kyara ke haifarwa ga mutane irinsu Misbahu, a cewar Dokta Bulus Yaksat, malamin Nazarin Halayyar Dan-Adam a Tsangayar Ilimi ta Jami'ar Abuja.

"[Tsangwama] kan iya sa mutum ya yi tunani daban-daban—[ya tambayi kanshi, 'Me ya sa na zo haka? Ko ya tambayi kanshi me ya sa Allah Ya yi shi haka".

Dokta ya kara da cewa, "Kai, tunani ma yakan iya shiga har ma mutum ya kasa cin abinci, ya kasa yin abin da zai taimaka wa kansa, ya kuma kasa yin abin da zai taimaka wa al'umma....

"Wannan tunani [kuma] zai iya sa mutum ma ya kashe kansa, ko ya gudu ya bar unguwarsa, ko iyalinsa, ko gidansa".

Matsayin Musulunci

Galibin al'ummar da Misbahu da iyayensa ke zaune a cikinsu Musulmi ne.

Amma Musulunci bai yarda da tsangwamar da Misbahu ya ce an nuna masa ba, a cewar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, malamin addinin Musulunci, kuma Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Image caption Mayar da mata-maza jinsi daya bai saba wa Shari'ar Musulunci ba, inji Shaikh Aminu Daurawa

Hasali ma, inji malamin, Musulunci ya yi bayani sosai a kan mas'alar mata-maza da kuma hukunce-hukunce game da su.

"Addinin Msulunci ya yi bayani kan yadda za a yi rabon gado ga mata-maza, da lamarin aure da na shugabanci, kuma addini bai yarda a dinga musguna musu ba tun da ba su suka halicci kansu ba," inji shi.

Malamin ya kara da cewa ta fuskar hukunce-hukunce, malaman Fikihu sun kasa mata-maza kashi uku: mai halittar mata da maza, amma ta mata ta fiyawa; da mai halittar mata da maza, amma ta maza ta fi yawa; da kuma mai halittar mata da maza, kuma dukkansu sun yi daidai da daidai.

"In an je likita ya tabbatar cewa wannan gaskiya mace ce—yana al'ada, zai iya daukar ciki—amma kuma wasu halittu da ake samu a jikin namiji sun fito masa—dabi'unsa da halayensa duk na namiji ne—to wannan sai a yi masa hukunci a matsayin namiji.

"A Shari'ance za a ba shi gadon namiji, sannan shi zai aura, sannan zai yi limanci, duk wasu abubuwa da ake yi na addini zai iya yi".

Shaikh Daurawa ya kara da cewa, "Kamata ya yi mutane su dinga jawo su a jiki tare da kwantar musu da hankali don kar su dauki matakin kashe kansu."

Yaya aka haihu a ragaya?

Image caption Babu alkaluman da ke nuna yawan mata-maza, amma Dokta Anas Yahaya ya yi kiyasin cewa a wani babban asibiti a Kano ana iya haifar daya a cikin haihuwa 2,000

A wasu kasashen gabashin Afirka, iyayen da suka haifi mata-maza kan dauka cewa an yi musu baki ne, don haka su kan kalli lamarin a matsayin abin kunya ko ma abin neman tsari.

Sai dai a cewar masana akwai bayani a kimiyyance game da yadda halittar mata-maza ke kasancewa.

Dokta Anas Yahaya, malami a Sashen Nazarin Halittar Dan-Adam da ke Jami'ar Bayero ta Kano, ya ce mata-maza halitta ce da ke samuwa sakamakon matsalolin sinadaran da ke taimakawa wajen haliita.

"Alal misali", inji shi, "lokacin da kwan namiji da na mace suka hadu suke ba da halitta ta namiji ko mace, to a lokacin ake samun matsala ta yadda kwan mace kafin ya hadu da na namiji ... kan rabe gida biyu; idan aka yi [rashin] sa'a maniyyin namiji guda biyu suka hadu da rababben kwan na mace, shi ke nan sai a samu mata-maza."

Masanin ya kuma ce ba gadon halittar ake yi ba, ko da yake akwai wadansu dalilan da kan haddasa ta baya ga rabewar kwan mace kafin haduwarsa da na namiji.

Sannan kuma, a cewar Dokta Yahaya, zai yi wuya a iya gane cewa jaririn da ke ciki mata-maza ne ta hanayr amfani da gwaje-gwajen da aka saba yi wa masu ciki—sai dai ta hanyar wani gwaji na musamman, inda za a debi ruwan cikin mai juna-biyu a auna.

Tiyata

Cigaban zamani dai ya zo da abubuwa da dama, ciki har da dabarun sauya halittar dan-Adam ko yi mata kwaskwarima.

Don haka ne ma idan mata-maza na sha'awa za a iya yi masa tiyata a mayar da shi namiji sak ko mace sak.

Kuma kamar yadda muka ambata tun da farko, mahaifan Misbahu sun je asibiti tun yana jariri, likitoci suka shaida masa cewa ana iya tiyata a mayar da yaron nasu namiji sak, amma sai ya yi kwari.

Sai dai kuma saboda rashin wadata, ba a iya yi masa aikin ba har sai da ya shekara 24.

Tuni dai, bayan samun tallafi daga al'ummar gari, an yi masa kashi biyu bisa uku na aikin da zai mayar da shi namiji sak.

"Zuwa yanzu an yi tiyata mataki biyu—ta farko an cire masa nonon da ke kirjinsa, ta biyu kuma an tsayar da haila—amma ba a cire masa al'aurar mata ba don kuwa har yanzu ba mu da isassun kudin yin hakan", inji Tunau.

Ya kuma kara da cewa, "Gaba daya abin da ake nema na aikin naira 250,000 ne. Ana kuma bukatar naira 70,000 don yin aiki na karshe amma wallahi kudin da muka samu ba su taka kara sun karya ba shi yasa har yanzu ba a kammala aikin ba".

Labarai masu alaka