Babbar mota ta kashe mutum fiye da 10 a Zariya

map

Rahotanni daga birnin Zariya na jihar Kaduna a arewacin Najeriya na cewa, wasu mutane sun rasa rayukansu bayan da wata motar tirela ta kwace daga hannun direban ta bi ta kan su a wata tashar mota da ke birnin.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa fiye da mutum 10 ne suka mutu a nan take a tashar motar wadda ke da cunkuson mutane a ko yaushe.

"Wata babbar mota ce ta tattake mutane bayan da ta kwace wa direbanta ta afka cikin mutane a wani wurin shiga mota da ke kan gadar," in ji wani ganau.

Al'amarin ya faru ne a daren ranar Lahadi.

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ba ta bayar da adadin yawan wadanda suka mutu ba.

Sai dai akwai fargabar cewa yawan wadanda suka mutun zai iya karuwa.

Wannan abu dai ya faru ne a kusa da gadar da ke hanyar Kano zuwa Kaduna, inda aka mayar tasha.

Ana yawan samun afkuwar hadurra a Najeriya, yawanci kuma sukan hada da manyan motoci wadanda ake dangantawa da matsalar burki.

A karshen watan Afrilu ma an yi wani mummunan hatsari a birnin tarayya Abuja, inda burki ya kwace wa wata babbar motar daukar yashi, inda ta bi ta kan wadansu motocin tasi biyu.

Mutane da dama ne kuma suka rasa rayukansu a hadarin.

Labarai masu alaka