Yadda Isra'ila 'ta karkashe' Falasdinawa

kimanin mutum 2,700 ne suka samu raunuka a tarzomar Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kimanin mutum 2,700 ne suka samu raunuka a tarzomar

Al'ummar Falasdinawa na shirin gudanar da sabuwar zanga-zanga ranar Talata kwana guda bayan dakarun Israila sun kashe mutane 58 a Gaza.

A ranar 15 ga watan Mayun ne kowace shekara ce ranar da Falasdinawa suka yiwa lakabi da Nakba, wato ranar da aka shaida mummunar bala'i .

A ranar ce dubban jama'a suka fice daga gidajen su yayin da aka kafa Israila a shekarar 1948 wanda ke cika shekaru 70.

An dai fuskanci tashe-tashen hankula ne sakamakon bude ofishin jakadanci Amurka a birnin Kudus, inda sojin Isra'ila suka budewa Falasdinawa masu zanga-zanga wuta.

Sai dai Firai ministan Israila Benjamin Netanyahu ya ce sojoji na kare kansu ne daga mayakan Hamas wanda ya ce suna son wargaza Israila.

Jami'an Falasdinawa sun ce baya ga wadanda aka kashe akwai kimanin mutum 2,700 da suka samu raunuka a tarzomar.

Ana kallon tarzomar a matsayin mafi muni a Gaza tun bayan yakin shekarar 2014.

Sauya wa ofishin matsuguni daga Tel Aviv dai ya yi matukar harzuka Falasdinawa wadanda ke kallon matakin da Amurka ta dauka a matsayin nuna goyon baya ga Israila na iko da birnin.

Tuni wasu kasashen duniya suka yi Allah-wadai da kashe kashen inda Kuwait ta bayyana abun daya faru a matsayin babban abun takaici.

Shin me yasa ofishin jakadancin ke janyo cece ku ce?

Hakkin mallakar hoto Raffi Berg
Image caption An rika sayar da hulunan Yahudawa masu hoton Trump a birnin Kudus

Kasashen duniya ba su amince da mamayar da Israila ta yi wa birnin Kudus ba kuma a yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma tsakanin Israila da Falasdinu a shekarar 1993 ya kamata a ce an yi magana game da makomar birnin a tattauanawar zaman lafiya da za a yi daga baya.

Tun daga shekarar 1967 ne Israila ta mamaye gabashin birnin Kudus lokacin da aka yi yaki a gabas ta tsakiya. Sai dai ba bu wata kasa da ta amince da haka sai lokacin da shugaba ya ayyana aniyyar kasarsa a watan Disambar shekarar 2017.

Tun daga shekarar 1967, Israila ta gina matsugunai da dama ga yahudawa 200,000 a gabanshin Kudus. Sai dai dokokin kasa da kasa ba su amince da matsugunan ba kodayake Israila na da ja da hakan.

Akwai wasu kasashe da suke da ofishohin jakadanci a birnin kudus amma daga baya sun tashi bayan da Israila ta amince da wata doka a shekarar 1980 da ta ayyana Kudus a matsyin babban birnin kasar

Shawarar da shugaba Trump ya yanke na amincewa da Kudus a matsayin babban birnin Israila ta sabawa matakin ba ruwa na Amurka da ta shafe shekaru da dama tana dauka kan batun kuma hakan ya sa ta samu sabani da kasashen duniya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karamin ofishin jakadancin Amurka da za a yi amfani da shi a matsayin ofishin jakancin kasar na wucin-gadi a birnin Kudus
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ivanka Trump ta gaisa da jakadan Amurka David Friedman kuma tana tare da mijinta Jared Kushner a filin jirgin sama na Ben Gurion

Labarai masu alaka