Kana son sanin tsawon shekarun da za ka rayu a duniya?

Adadin shekarun da mutane kan rayu a duniya na karuwa. Mutanen da aka haifa a shekarar 2016, ana hasashen a taikaice za su yi tsawon rai fiye da wadanda aka haifa shekara 25 da ta gabata.

Sai dai akwai wasu abubuwa da ke taka muhimmiyar rawa a tsawon shekarun da mutum zai iya yi a duniya wadanda suka hada da kasar da mutum ya ke da kuma jinsinsa.

BBC ta tsara wannan ma'aunin da zai ba ku damar sanin hasashen tsawon shekarun da za ku yi a duniya.

A don haka mai zai hana ku jarraba wa:

Kiyasi kan tsawon rai a duniya tun daga haihuwa shi ne shekara 72, wato 70 ga Maza 75 kuma ga Mata. Amma a kan samu sauyi saboda shekaru. Misali, Wanda ke da shekaru 69 na iya kara yin wasu shekaru 17.

Hanyoyin da aka bi wurin hada rahoton

Wadannan sabbin alkalumma ne da aka fitar a 2016. Wannan ya shafi hasashen adadin shekarun da mutum zai yi a duniya bisa la'akari da shekarunsa da jinsinsa da kuma kasarsa.

Yaya tsawon rayuwarku za ta kasance cikin koshin lafiya, ana kiyastawa ne daga yawan shekarun da ake hasashen mutum zai yi cikin koshin lafiya, wanda aka nuna a matsayin hasashen adadin shekarun da suka rage.

Labarai masu alaka