Mata sun yi zanga-zanga kan hana mace shayarwa a kantin cin abinci

kenya Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wasu mata masu cike da fushi a Kenya, sun yi zanga-zanga a wani kantin sayar da abinci da ke Nairobi babban birnin kasar, domin nuna fushinsu kan abun da suka kira 'wulakancin' da aka yi wa wata mata mai shayarwa.

Matan sun je kantin cin abinci mai suna Olive, inda a can ne matar ta yi zargin cewa an hana shayar da 'yarta mai shekara daya.

Matar, wadda ta bayar da labarin wanan lamarin a wani shafi na iyaye mata a Facebook, ta bayyana cewa an matsa mata dole ta shiga ban-daki don shayar da 'yarta, inda hakan ya yi matukar bata mata rai kuma ya zama wulakanci.

Wanan labarin ya yadu sosai a Nairobi da ma wasu wuraren, wanda ya sa aka shirya yin zanga-zanga zanga da safiyar ranar Talata.

Jaridar Daily Nation ta wallafa bidiyon zanga-zangar a shafinta na Twitter, wadda aka fara ta daga Freedom Corner kafin daga bisani zu je majalisar dokoki su kuma wuce kantin sayar da abincin.

Shugabannin gidan cin abincin sun yi kira da a kwantar da hankali yayin zanga-zangar matan, sun kuma roki a dan ba su lokaci kadan don daukar matakin da ya dace.

'Bazan iya shayarwa a cikin ban daki ba'

Ms kim ta gaya wa BBC cewa ma'aikatan wajen sun taso ta gaba bayan da ta fara shayar da 'yar tata.

"Ina cikin jiran abincin da na siya na miyar nama da kabeji nikakken dankali, sai kawai wata ma'aikaciyar wajen mara mutunci wadda ta na umarta ta kawo min abincin, ta zo ta ce min in daina shayarwa ko in rufe jikina."

"Na kadu sosai da jin hakan saboda na sha shayarwa a cikin mutane, sannan kuma a wannan ranar ma ruwan sama akenyi, don haka ba inda zan je na fake."

Ms Kim ta ce 'yarta tana ta faman kuka don haka ba ta da mafita sai dai ta ba ta nono.

"Na yi tunanin cewa bari kawai in ci gaba da ba da nonon sai wannan ma'aikaciyar daban ta ce abin da nake ba kyau.

"Sai na tambaye ta cikin kwanciyar hankali cewa to a ina take so na je na shayar da 'yata, sai kawai ta nuna min bandaki.

"A lokacin sai na ji na muzanta har na daina ba da nonon."

A yanzu Ms Kim tana fatan shugaban kantin ya ba ta hakuri a kan abin da ya faru.

Labarai masu alaka