Auren masarautar Birtaniya 2018: Yarima Harry da Meghan Markle

Yerima Harry Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yerima Harry da Meghan Markle

A ranar Asabar, 19 ga watan Mayu da misalin karfe 12 rana za a daura wa Yerima Harry da Meghan Markle aure a cocin St George da ke Windsor, inda nan ne aka daura auren Yerima Peter Philips da Autumn Kelly a shekarar 2008.

Shawarar da masoyan suka yanke na yin aure a ranar Asabar ta sabawa al'ada, saboda 'ya'yan masauratar Birtaniya sun fi yin aure a cikin mako, ba karshen mako ba.

A ranar Juma'a ce aka daura wa Duke da kuma Duchess na Cambridge watau Yarima William da Catherine Middleton aure kuma a ranar Alhamis ce aka daurawa sarauniya Elizabeth aure

A ranar ce kuma za a yi gasar cin kofin kwallon kafa ta FA a filin Wembley, wasan daYerima William, wanda shi ne shugaban kungiyar kwallon kafa ta kasar ya ke halarta domin ya bada kofi ga kugiyar da ta yi nasara.

Duk da cewa an ba ma'aikata hutu a ranar da Yarima Charles ya auri Diana Spencer a 1981, da ranar auren Yarima William da Catherine Middleton a 2011, da kuma ranar auren gimbiya Anne da Mark Phillips a shekarar 1973,ranar da Yarima Harry da Meghan suka zaba domin yin aure ya kawar da da duk wani surutu da ake yi a kan ko ya kamata a bada hutu a ranar auren ko kuma aa.

Shin wanene HARRY?

Shi ne autan mai martaba Yarima Charles da marigayayi gimbiyar Wales Diana, kuma Yarima Harry shi ne na shida a jerin wadanda za su gaji saurauta tun bayan da aka haifi gimbiya Charlotte.

A ranar 15 ga watan Satumba ta shekarar 1984 ne aka haifi Yarima Harry a asibitin St. Mary da ke Paddington a birnin Landan, inda yanzu shekarasa 33.

Sai dai duk da cewa an fi sninsa da Harry ,amma Henry Charles Albert David na yankin Wales shi ne cikakken sunansa , a kan haka a hukumance shi ne yerima Henry na Wales'

Yarima Harry ya halarci makarantar Mrs. Mynors, da yanzu ta koma Wetherby da ke birnin London kafin daga bisani ya je wurin da yayansa ya ke karatu watau makarantar Ludgrove da ke Berkshire kafin ya wuce kwalejin Eton.

Bayan da bar makaranta, ya yi aiki a kungiyoyin masu zaman kansu daban-daban a kasashen Australia da Argentina da kuma nahiyar Afrika.

Bayan da ya dawo gida ya wuce kwalejin horas da sojoji ta Sandhurst.

Yana goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal kuma ana ganinsa a wassannin da kungiyar ke bugawa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fadar Kensington

Shin wacece Amaryar?

A ranar 4 ga watan Augusta ta shekarar 1981 aka haifi Meghan Markle, wadda jaruma ce a wasan kwaikwaiyon da ake nunawa ta kafar talabijin a Amurka.

Ta girma a Los Angeles kafin daga baya ta koma da zama birnin Toronto.

Iyayen Meghan sun rabu ne lokacin da ta ke da shekara shida.

Ta yi karatu a wata makarantar Firamare mai zaman kanta kafin ta wuce kwalejin mata na cocin darikar katolika. Daga bisani ta kammala karatun digiri a jami'ar Northwestern inda ta karanta aikin sadarwa a shekarar 2003.

Wasan kwaikwayo na farko da ta fara fita a Amurka shi ne "General Hospital"a shekarar 2002.

Ta kuma fito a wasannin kwaikwayo na "CSI" da"Without a Trace" da "Castle".

Ta fito a wasu fina-finan Hollywood da suka hada da "Get Him to the Greek" da "Remember Me" da kuma "Horrible Bosses".

Wannan dai ba shi ne auren Miss Meghan na farko ba - a shekarar 2011 ta auri Trevor Engelson wanda furodusa ne na fim amma bayan shekara biyu da aure suka rabu.

Banbancin shekaru

Meghan ta girmi Yarima Harry wanda za ta aura mijinta da shekara uku. A ranar 4 ga watan Augusta aka haife ta a shekarar 1981, yanzu shekararta 36.

A ranar 15 ga watan Satumba na shekarar 1984 aka haifi Yarima Harry, yanzu shekararsa 33.

Akwai tazarar shekara 13 tsakanin mahaifiyarsa gimbiya Diana da kuma mahaifinsa Yerima Charles.

Su wanene zasu halarci daurin auren?

Mutune 600 aka tura wa goron gayyata, kuma an tura wa karin mutane 200 da goron gayyata domin halartar liyafar cin abincin da aka shirya wa ango da amaryarsa da za a yi a da yamma, ciki har da Spice Girls, da suka yi fice a fagen waka.

Sai dai yawan mutanen da aka turawa goron gayyata bai kai yawan wadanda suka halarci daurin auren Yarima William da kuma Kate ba, inda aka daura auren a gaban baki dubu 1,900.

Ko da yake adadin bai kai na bakin da suka halarci daurin auren sarauniya Elizabeth ta biyu da kuma Yarima Philip ba wadanda suka gayyaci baki 2,000 a daurin aurensu da aka yi a shekarar 1947.

Iyayen Meghan, watau Thomas Markle da Doria Ragland, za su isa Birtaniya a makon da mu ke ciki domin su gana da sarauniya da Yarima Charles da kuma sauran 'yan uwa da abokan arziki.

Fadar Kensington ta tabbatar da cewa mijin sarauniya, zai halarci daurin auren duk da cewa a yana murmure daga aikin da aka yi ma sa a kwankwaso.

Dukkanin yan uwan mahaifiyarsa su uku za su je daurin aure watau Lady Jane Fellowes, da Lady Sarah McCorquodale da kuma Earl Spencer.

Firaministar Birtaniya Theresa May da kuma jagoran 'yan hamayya Jeremy Corbyn ba sa cikin bakin da aka tsara za su halarci daurin auren, wannan ya biyo bayan matakin da aka dauka a kan cewa a hukamance ba za a fitar da sunayen 'yan siyasa da aka turawa goron gayyata .

Fadar Kensington ta ce matakin na nufin cewa shugaba Donald Trump na Amurka ba zai halarci daurin auren ba, kuma an yanke wannan shawara ce bayan da aka tuntunbi gwamnatin kasar, kuma an yi haka ne saboda an yi la'akari da cewa shi ne na shida a jerin masu jiran sarauta a Birtaniya.

An kuma tabbatar da cewa Barack da Michelle Obama, wadanda abokan Yarima Harry ne ba su sami goron gayyata ba.

Amma akwai yiyuwar cewa shahararriyar 'yar wasan Tennis Serena Williams, da kuma makwaki Elton John da tsohon dan wasan kwallon kafa David Beckham za su halarci daurin auren.