Majalisa ta amince da kasafin kudin Najeriya na 2018

Buhari a majalisa Hakkin mallakar hoto Reuters

Majalisar dokokin Najeriya ta amince kasafin kudin kasar ta shekarar 2018.

Wannan ya zo ne a lokacin da majalisar ta kara kasafin kudin da kasar za ta kashe zuwa naira triliyan 9.1 daga naira triliyan 8.6.

A watan Nuwamban shekarar 2017 ne dai Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban majalisar.

Kasafin kudin da majalisar ta mince da shi ya fi naira triliyan 8.6 da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar ga majalisar a watan Nuwamba.

'Yan majalisa dai sun ce an kara kasafiun kudin domin hasashen da ake yi na cewa kudin gangar danyen mai zai karu zuwa $51, sama da dala 45 da ke cikin kasafin kudin da Shugaba Buhari ya gabatar, in ji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Amma nan gaba sai an mayar da kasafin kudin ga Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kansa kafin ya zama doka.

Bangarorin da za a fi kashewa kudi a kasafin

A karkashin kasafin kudin na bana, ma'aikatar Wutar Lantarki, Ayyuka da Gidaje ce ta sami kaso ma fi tsoka na Naira biliyan 555.88.

Shugaba Buhari ya bayyana dalilin ba wannan ma'aikata kaso mai yawa: "Gwamnati na son samar da sabbin ayyuka da za su kawo cigaban tattalin arziki da raya kasa."

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ce ke ta biyu, inda aka ware mata Naira biliyan 510.87, daga nan sai ma'aikatar Ilimi da zata sami Naira biliyan 435.01.

Daga nan kuma sai ma'aikatar Tsaro da zata sami Naira biliyan 422.43, sai ma'aikatar Kiwon Lafiya da aka ware mata Naira biliyan 269.34.

Ma'akatar Sufuri an ware mata Naira biliyan 263.10, inda aka ba ma'aikatar Noma da Raya Karkara Naira biliyan 118.98.

Sai kuma ma'aikatar Albarkatun Ruwa da za ta sami Naira biliyan 95.11, sai kuma ma'aikatar Ma'aikatu da Cinikayya da Zuba Jari mai kason Naira biliyan 82.92

Amma ana sa ran gibin dake tsakanin kasafin kudin shiga da ainihin wadanda za su shiga lalitar gwamnati zai ragu daga Naira tiriliyan 2.36 na kasafin kudin bara zuwa 2.005 a kasafin kudin bana.

Kasafin kudin dai zai zama doka ne kawai idan 'yan majalisar kasar suka amince da shi.

Bangaren gwamnati da na majalisa sun sha kai ruwa rana kan kasafin kudi musamman wanda ya gabata, al'amarin da har ya kai ga tonon silili tsakanin 'yan majalisar.

Labarai masu alaka