'Yan matan da ake bayar da su ga ababen bauta
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan matan da ake bayar da su ga ababen bauta a Ghana

Latsa alamar hoton da ke sama don kallon bidiyon:

An shafe daruruwan shekaru ana bautar da dubban mata a fadin Afirka ta Yamma ta hanyar bin wata al'ada da ake kira Trokosi.

Brigitte Sossou Pereny na daya daga cikin irin wadannan 'yan mata, har sai zuwa lokacin da wani Ba-Amurke ya dauke ta ya mayar da ita Amurka.

Bayan shekara 20 Brigitte ta koma kasarta don yin bincike akan dalilin da ya sa ake al'adar Trokosi, a karkashin wani sashen binciken kwakwaf na BBC Afirka, don sanin dalilin da ya sa danginta suka bai wa abun bauta ita.

Labarai masu alaka