Cutar Ebola ta yadu har zuwa birnin Mbandaka

Jami'an kiwon lafiya a asibitin Biokoro na DR Congo

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

An tura Jami'an kiwon lafiya yankin da cutar ke yaduwa domin ceto rayuka

Ma'aikatar lafiya a Jamhuriyar Demokradiyar Congo ta ce an sake samun masu dauke da cutar Ebola a birnin Mbandaka da ke arewa maso yammacin kasar.

Akwai miliyoyin mutane da ke rayuwa a yankin, kuma samun masu dauke da cutar na bayyana yadda ta ke yaduwa a wani sabon yanayi cikin gaggawa.

Mutum 23 aka bada rahotan mutuwarsu tun sake bullar cutar a farkon wannan watan na Mayu, a wani kauye mai nisan kilomita kusan 150 da garin na Mbandaka.

Wannan dai shi ne karo na 9 da ake samu bullar Ebola a Congo tun shekara ta 1967.

A cewar ministan lafiyar kasar, Oly Ilunga Kalenga tun a jiya Laraba, hukumar lafiya ta Majalisar Duniya Duniya ta aike da dubban alluran rigakafi na gwaji zuwa kasar.

''Ya ce za ayi wa mutane da suka yi mu'ammala da masu dauke da cutar, da wadanda ma ba sa dauke da cutar allurar rigakafin, gida-gida za a bi domin gudanar da wannan aiki don ceto rayuka.''

Ana dai yi nasara a gwajin alurar rigakafin da aka yi bayan yaduwar Ebolar a wasu kasashen yammacin Afirka daga shekara ta 2014.

Cutar dai ta kashe fiye da mutum dubu 11 a yammacin Afrikan a 2014.

Asalin hoton, AFP/getty

Bayanan hoto,

Mutum 23 sun mutu zuwa yanzu a DR congo