Burundi: Nkurunziza na neman wa'adi na shekara 7

Picture of Burundi President Pierre Nkurunziza Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun shekarar 2005 Pierre Nkurunziza ke mulkin kasar Burundi

Mutanen Burundi na shirin jefa kuri'a a wani zaben raba grdama da ke cike da takardama, kuma zaben na iya ba Shugaba Pierre Nkurunziza damar tsawaita mulkinsa har shekara ta 2034.

Ga dalilan da ya sa zaben ke cike da matsaloli a kasar:

Wanene Shugaba Nkurunziza?

Nkurunziza tsohon jagoran wata kungiyar 'yan tawaye ne wanda ya dare karagar mulkin kasar Burundi bayan yakin basasar kasar da ya kare a 2005.

Takarar da ya tsaya ta neman shugabancin kasar a shekarar 2015 ta janyo tashin hankali da rikicin siyasa da kuma yunkurin juyin mulki da sojojin kasar suka dakile.

Wannan rikicin ya kuma janyo mutuwar daruruwan mutane, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta ce fiye da mutum 400,000 sun tsere daga kasar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana nuna wa 'yan Burundi cewa shugaban mai son jama'a ne

Dalilin gudanar da zaben raba gardama

'Yan Burundi za su kada kuri'ar suna so, ko basa son a tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa daga shekara biyar zuwa shekara bakwai.

A yanzu ana amfani da tsarin wa'adin shugabanci sau biyu ne ga shugaban kasa.

Amma wannan sauyin na iya ba Mista Nkurunziza damar sake tsayawa zabe a shekarar 2020, kuma yana iya sake maimaita wa'adin a karkashin sabuwar dokar domin za a manta da wadancan shekarun da ya shafe yana mulki.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutum 400,000 ne suka tsere daga Burundi a 2015

Labarai masu alaka

Karin bayani