Amsoshin tambayoyinku kan rikicin Iran da Isra'ila

  • Daga Jonathan Marcus
  • Wakilin BBC kan Tsaro da Diflomasiyya
Israeli Merkava tanks and soldiers near the Syrian border in the Israel-annexed Golan Heights

Asalin hoton, AFP

Ana ci gaba da fuskantar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, bayan Isra'ila ta kai wa Iran hari da makami mai linzami a Syria, a matsayin martani ga harin rokoki da aka kai a yankin Golan Heights da Isra'ilar ta mamaye.

Kasashen duniya da dama sun yi Allah-wadai da harin rokokin, wanda Isra'ila ta zargi Iran, kamar yadda Amurka ta zargi Iran da kokarin haifar da yaki a Gabas ta Tsakiya.

To ko me zai iya faruwa nan gaba a yankin, me ya sa kasashen ke rikici da juna. Wakilin BBC da ke aiko da rahotanni kan diflomasiya Jonathan Marcus, ya amsa wasu daga cikin tambayoyin da galibi kuka aiko.

Me ya sa ake rikici tsakanin Isra'ila da Iran?

Ko shakka babu Iran kasa ce da ke kyamar Isra'ila, kuma da ke kokarin ganin an kawar da Yahudawa. Iran tana goyon bayan wasu kungiyoyin da suka dade suna adawa da Isra'ila, amma yanzu saboda yakin Syria, Iran ta samu damar kai wa ga iyakokin Isra'ila.

Samun nasarar shugaban Syria Bashar al Assad, yanzu babbar dama ce ga Iran.

Iran na kara samun karfi a Gabas ta Tsakiya. Tana kokarin tabbatar da tasirin karfin sojinta a Syria. Wannan kuma ya bambanta da shirin nukiliya, wani bangare ne da ya kasance babbar barazana ga Isra'ila.

Bayanan bidiyo,

Kafar Talabijin ta Syria ta nuna yadda Isra'ila ta kai hari a Damascus

Ko Isra'ila za kai hari Tehran idan har Iran ta kammala mallakar makaman kare-dangi?

Batun nukiliyar Iran na sake ruruwa, domin tun kafin yarjejeniyar nukiliyar Iran da Trump ya yi watsi da ita, Isra'ila da Iran suka kama hanyar abka wa cikin yaki, yayin da ake fargabar Isra'ila da Amurka na iya kai hari cibiyar nukiliyar Iran.

Me kasashen duniya suke domin hana ruruwar rikicin?

Yayin da kowa ke nuna damuwa tare da kiran a kai zuciya nesa da yin taka-tsantsan, wasu kasashen daga waje tasirinsu yana da iyaka. Isra'ila da Iran na kan hanyar gwabza yaki da juna.

Rasha wadda daya ce daga cikin kasashen da ke taka rawa a rikicin Syria, ta yi biris da yadda Isra'ila ke amfani da sararin samaniyar Syria, saboda tana ganin ba nata ba ne, lamarin da ya saba wa bukatun Iran a Gabas Ta Tsakiya.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da shugaban Amurka Donald Trump sun taba ganawa a Washington a watan Maris na 2018

Amurka kuma ta rage karfin fada ajin da take da shi a yankin, yayin da Shugaba Trump ya fi karkata da nuna goyon baya ga Isra'ila.

Shin Isra'ila ce ke takalar fada?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Wakilin BBC ya ce ba shi da masiniya game da wannan. Amma ga alama Isra'ila tana hannunka mai sanda ne ga Iran ta sauya tunani. Iran tana kallon abubuwan da Isra'ila ke yi a Syria a matsayin takalar fada.

Isra'ila na adawa da rawar da sojojin Iran ke takawa a kan iyakokinta.

Baya ga MDD da NATO, wa Birtaniya za ta goyi baya a rikicin Isra'ila da Iran?

Ba ni da wani tabbas game da "goyon baya na hakika". Amma ko shakka babu Birtaniya ba ta jin dadin rawar da Iran ke takawa a yankin da kuma fargaba game da shirin nukiliya.

Sai dai ba kamar Amurka ba, Birtaniya tana son ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliya da aka kulla da Iran.

Wakilin BBC ya ce yana ganin kusan dukkanin gwamnatoci da wasu hukumomi na kasashen duniya za su yi kokarin guje wa duk wani rikici tsakanin Isra'ila da Iran.

A martanin da Birtaniya ta mayar a harin daren Laraba, sakataren harakokin wajen kasar Boris Johnson ya ce: "Birtaniya ta yi Allah-wadai da harin roka da Iran ta kai kan sojojin Isra'ila. Mun goyi bayan Isra'ila ta dauki matakan kare kanta."

Ya bukaci Iran ta kaucewa duk wani abun da zai kara haifar da matsalar tsaro a yankin.

Ko akwai tattaunawa da aka taba yi tsakanin Isra'ila da Iran?

Wakilin BBC ya ce zai yi mamaki idan har akwai wata tattauna ta kai-tsaye da aka yi.

Wani lokaci wasu ke shiga tsakani - misali kamar Rasha - amma "sako" daga Isra'ila zuwa ga Iran, ana gabatar da shi ne a fili kai-tsaye.

A zamanin Sarkin Iran Mohammed Reza Shah, akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin Isra'ila da Iran.

An rusa dangantakar ne bayan juyin juya halin musulunci a 1979, ko da yake an yi tunanin Isra'ila za ta ci gaba da sayar wa da Iran da makamai a yayin da take yaki da Iraki. Daga baya dangantakar kasashen biyu ta kara rincabewa.

Manufofin Iran dai na da karfi ga kyamar Isra'ila da Yahudawa.

Iran ta inganta karfin soji sosai, ba wai ga mayakan Hezbollah na Lebanon ba, ana ganin ta tallafa wa kungiyoyi masu dauke da makamai domin yakar Isra'ila da Yahudawa - zargin da Iran ta sha musantawa.