Hamshakin attajirin Najeriya ya shiga bas da talakawa

Femi Otedola Hakkin mallakar hoto Instagram/@FemiOtedola

Ana yada bidiyon attajirin dan kasuwan Nigeriya, Femi Otedola, a shafukan sada zumunta bayan ya shiga motar bas tare da talakawa a jihar Legas.

A cikin bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram na Mista Otedola a ranar Laraba, an gano biloniyan tare da fasinjoji a cikin wani tsohon bas wanda ake kira "Molue".

Hakkin mallakar hoto Instagram/FemiOtedola
Image caption Ko watan jiya ma attajirin ya hau bas a birnin Landan domin ya je ya gai da tsohon malaminsa

Yana tafiya ne daga unguwar Sango zuwa Agege a birnin kasuwancin na Najeriya, Legas, bisa ga bayanin da aka wallafa tare da bidiyon.

Babu wani fasinja da ya gane biliyoniyan har sai bayan da ya sauko daga motar.

Bidiyon da aka wallafa a shafin Instagram na Mista Otedola bai bayyana dalilin da ya sa ya hau bas din ba, amma mutane da yawa sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu game da bidiyon a kan shafin Twitter:

Labarai masu alaka