Za a baje kolin takalmin Mohamed Salah

Za a baje kolin takalmin Salah
Image caption Za a baje kolin takalmin Salah tare da mutum-mutumi na sarakunan Masar da kuma sauran kayan kufai

Gidan adana kayan kufai da aka tattaro daga Masar na Birtaniya zai baje kolin takalmin kwallon kafa na dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah.

Zaa baje kolin takalminsa ne gabanin karawar da Liverpool za ta yi da Real Madrid a wasan karshe na gasar zakarun Turai, wanda za a yi a ranar 26 ga watan Mayu.

"Takalmin kwallon kafar za su ba da labarin shahararen dan wasan kwallon kafa da ya fito daga Masar, wanda ya ja hankali sosai a Birtaniya da kuma duniya baki daya", in ji Neal Spencer jami'i a gidan adana kayan kufai na Birtaniya.

Bajintar da dan wasan kwallon kafa na Masar ya nuna a kakar wasanni ta bana ta sa an ba shi kyautar wanda ya fi cin kwallo a duniya bayan kwallaye 32 da ya zura a raga.

Labarai masu alaka