Hotunan muhimman abubuwan da suka faru a Afirka a makon jiya

Wasu daga cikin hotunan abubuwa mafi kyau da suka faru a wurare daban-daban na Afirka da 'yan Afrika awasu wurare a duniya a makon da ya gabata.

A girl ties the Palestinian Kiffeyyah during a demonstration of members of pro-Palestinian groups and other civil society groups outside the US Consulate General in Sandton district of Johannesburg, on May 15, 2018, to protest against the killing, the day before, of 59 Palestinians in clashes and protests Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan Afirka ta Kudu sun taru a wajen ofishin jakadancin Isra'ila a birnin Johannesburg ranar Talata, don nuna rashin amincewa da mutuwar Falasdinawa masu zanga-zanga.
A protester carries a doll as she and others march towards a restaurant after a female client was allegedly thrown out for breastfeeding and not covering up in Nairobi"s Central Business District on May 15, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu mata 'yan Kenya sun taru a titunan birnin Nairobi domin yin Allah-wadai da hana wata mata shayar da jaririnta a wani kantin cin abinci.
People navigate the the waterways of Makoko waterfront community in Lagos on May 15, 2018. Members of various waterfront communities and the Nigerian Slum/Informal Settlement Federation have protested on the day marking one year anniversary of the forced eviction of the Otodo Gbame community, a Lagos shanty town, Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A wani bangaren nahiyar Afirka, masu fafutuka a birnin Lagos na Nigeria sun yi zanga-zanga bayan cika shekara daya da aka tilasta musu barin yankin Otodo Gbame - da a baya suke rayuwa a gabar teku.
A man pushes a wheelbarrow through the streets as Somaliland celebrates its independence Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata kuma, mutane sun yi bikin shekaru 27 na samun 'yancin kan da Jamhuriyyar Somaliland ta ayyana kanta, kwanaki uku kafin a fara azumin Ramadan.
A supporter of Kenya's Gor Mahia poses before the friendly football match Kenya"s Gor Mahia vs England"s Hull City at the Kasarani stadium in Nairobi on May 13, 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane sun kasance cikin annashuwa a birnin Nairobi na Kenya, a ranar Lahadi, yayin da 'yan wasan kwallo Gor Mahia suka buga wasan sada zumunici da 'yan wasan kungiyar Hull City ta Ingila.
Zimbabwe War veterans sing and dance ahead of a consultative meeting between the veterans of Zimbabwe"s liberation war and leaders of Zimbabwe ruling party Zimbabwe African National Union Patriotic Front (ZANU PF) in Harare on May 11, 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Juma'a, 'yan mazan jiya na Zimbabwe sun yi ta rawa da waka kafin taron tattaunawa da shawarwari na Jam'iyyar Zanu-PF.
Supporters cheer for Union for the Republic and Democracy (URD) leader Soumaïla Cissé at a rally during the launch of his presidential bid in Bamako on May 12, 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Talata a Mali, Shugaban kungiyar adawa na Jam'iyyar Republica da democradiyya (URD), Soumaila Cisse, ya kaddamar da aniyyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a wani babban gangami.
A woman casts her vote at a polling station in Ciri, northern Burundi, on May 17, 2018 during a referendum on constitutional reforms that, if passed, will shore up the power of incumbent President and enable him to rule until 2034. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Alhamis ne, mutanen Burundi suka kada kuri'a don yanke shawara a kan sauya kundin tsarin mulki- wanda zai bai wa shugaban kasa, Pierre Nkurunziza ci gaba da kasancewa a mulki har 2034.
Burundian singer and member of the Feature Film Jury Khadja Nin arrives on May 16, 2018 for the screening of the film "Burning" at the 71st edition of the Cannes Film Festival in Cannes, southern France. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kwana guda kafin a yi wannan, wata mawakiya a Burundi Khadja Nin ta ja hankalin mutane yayin da ta hau jar daddumar da aka shimfida wa baki a bikin Cannes, a Faransa.

Hakkin mallakar hotuna AFP da Getty Images da Reuters da EPA.

Labarai masu alaka

Labaran BBC