Gina Haspel: Mace ta farko da za ta shugabanci CIA

Haspel Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gina Haspel ta jagoranci wata cibiya ta sirri da aka rika gallazawa wadanda ake tsare da su azaba

Majalisar Dattijan Amurka ta amince da nadin mace ta farko a matsayin shugabar hukumar leken asiri ta CIA duk da rawar da ta taka na jagorantar gallazawa wadanda ake tsare da su azaba.

Amma anyi gumurzu tsakanin 'yan majalisar bayan da aka yi ta sukar shirin gallazawa wadanda ake tsare da su a lokacin mulkin shugaba George W Bush.

'Yan majalisar sun kada kuri'u 54-45.

Gina Haspel tsohuwar ma'aikaciyar CIA ce wadda ta taba jagorantar wata cibiyar sirri da ke Thailand bayan hare-haren 11 ga watan Satumbar 2011.

Za ta maye gurbin Mike Pompeo wanda a yanzu shi ne sakataren harkokin wajen Amurka.

Sanata John McCain - wanda dan jam'iyyar Republican ne, wanda kuma aka taba azabtar da shi na fiye da shekara biyar - a lokacin da ake tsare da shi wani kurkukun kasar Vietnam ya soki nadin matar.

A ranar Alhamis sanatoci shida 'yan jam'iyyar Democrat suka goyin bayan 'yan Republican, dalilin da ya sa ta sami hayewa.

Labarai masu alaka