Mata-maza zai iya aure - Sheikh Daurawa
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mata-maza za su iya aure har da haihuwa - Sheikh Daurawa

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakkiyar hirar da Halima Umar Saleh ta yi da shaikh Aminu Daurawa.

Mata-maza mutane ne da ake haifarsu da al'aurar maza da kuma ta mata.

A wasu kasashen gabashin Afirka, iyayen da suka haifi mata-maza kan dauka cewa an yi musu baki ne, don haka su kan kalli lamarin a matsayin abin kunya ko ma abin neman tsari.

Mas'alar mata-maza al'amari ne mai sarkakiya, amma kuma tuni addinin musulunci ya tanadi hukunce-hukunce kan hakan sannan kuma bai yarda da tsangwamar da ake nuna wa mata-maza ba, a cewar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, malamin addinin Musulunci, kuma Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano.

Mayar da mata-maza jinsi daya bai saba wa Shari'ar Musulunci ba, inji Shaikh Aminu Daurawa

Hasali ma, inji malamin, Musulunci ya yi bayani sosai a kan mas'alar mata-maza da kuma hukunce-hukunce game da su.

"Addinin Msulunci ya yi bayani kan yadda za a yi rabon gado ga mata-maza, da lamarin aure da na shugabanci, kuma addini bai yarda a dinga musguna musu ba tun da ba su suka halicci kansu ba," inji shi.

Malamin ya kara da cewa ta fuskar hukunce-hukunce, malaman Fikihu sun kasa mata-maza kashi uku: mai halittar mata da maza, amma ta mata ta fiyawa; da mai halittar mata da maza, amma ta maza ta fi yawa; da kuma mai halittar mata da maza, kuma dukkansu sun yi daidai da daidai.

"In an je likita ya tabbatar cewa wannan gaskiya mace ce—yana al'ada, zai iya daukar ciki—amma kuma wasu halittu da ake samu a jikin namiji sun fito masa—dabi'unsa da halayensa duk na namiji ne—to wannan sai a yi masa hukunci a matsayin namiji.

"A Shari'ance za a ba shi gadon namiji, sannan shi zai aura, sannan zai yi limanci, duk wasu abubuwa da ake yi na addini zai iya yi".

Shaikh Daurawa ya kara da cewa, "Kamata ya yi mutane su dinga jawo su a jiki tare da kwantar musu da hankali don kar su dauki matakin kashe kansu."

Labarai masu alaka