Priyanka Chopra na halartar bikin masarautar Birtaniya

Priyanka Chopra Hakkin mallakar hoto Indian Express

Jaruma Priyanka Chopra ta isa birnin Landan domin halartar kasaitaccen bikin masarautar Birtaniya da za a yi a ranar Asabar, 19 ga watan Mayun, 2018 na Yarima Harry da amaryarsa Meghan Markle.

Priyanka wadda ta zazzaga wasu kasashen duniya a kwana-kwanan nan domin wasu aikace-aikace, da kuma hutun da taje tare da mahaifiyarta dama 'yan uwanta, ta isa birnin na Landan ne a ranar Jumma'a.

Jarumar ta ce tana ganin amaryar wato Meghan Markle, zata zamo gimbiya ta kowa.

Priyanka Chopra ta taba bayyana cewa sun taba haduwa da amarya Meghan a wajen wani taro shekara uku zuwa hudu da ta wuce, kuma sun shaku sosai.

Sannan ta ce sun taba haduwa a lokacin da ta je shirin fim a Canada, inda itama Meghan din taje shirin nata fim din.

Priyanka ta kuma rubutawa amaryar wata 'yar karamar wasika a mujallar Time, a lokacin da ta fito a ciki.

Bayan isarta birnin na Landon, jarumar ta dauki hoton kanta ta leka taga ba tare da kwalliya ba tana shan hantsi, inda ta wallafa a shafinta na instagram.

Priyanka dai zata kasance a bangaren kawayen amarya a wajen bikin.

Yanzu haka dai magoya bayanta na ta zumudin ganin irin kwalliyar da wannan jaruma zata sheka a wajen kayataccen biki na masarautar Birtaniya.

Priyanka Chopra, shahararriyar jarumar fina-finan Indiya ce, wadda kuma ta ke fitowa a wasu fina-finan na kasashen turai.

Kazalika, ta taba cin gasar sarauniyar kyau ta duniya, wato Miss World a shekarar 2000.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Daga cikin fina-finanta da suka yi fice akwai, Aitraaz da Barfi da Gunday da Krishh da Don da kuma Fashion.

Labarai masu alaka