Me ya sa babu wanda ya damu da rikicin Zamfara?

Zamfara

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Zamfara ta dade tana fama da rashin shugabanci nagari

Daga cikin jerin wasikun 'yan jarida daga Afrika, Kadaria Ahmed ta duba matsalar rikicin jihar Zamfara a Najeriya, wanda masana suke ganin zai iya yin kama da tashin hankalin da aka gani a rikicin Boko Haram.

A tasowata kusan shekaru 50 da suka gabata a jihar Zamfara yankin arewa maso yammacin Najeriya, ban taba tunanin makomar yankin za ta kai ga matsanancin talauci da tashin hankali ba.

Gusau babban birnin jihar Zamfara, ya kasance gari mai wadata. Kamfanin Birtaniya John Holt, yana da cibiya ta tattara fata da gyara domin fitar wa zuwa Turai.

Akwai cibiyar kamfanin sikari ta Tate & Lyle na Birtaniya. Sannan akwai babban kamfanin masaka da kamfanonin gurzar auduga da kuma kamfanin gurzar gyada domin samar da mai da kuli-kuli.

Lokacin da muna yara, wurin da muka fi sha'awa shi ne kamfanin minti da wasu 'yan kasar Lebanon suke yi, wanda a lokacin ke gamsar da bukatunmu da 'yan kudaden da muke da su.

Akwai babbar tashar jirgin kasa da ke jigilar kaya zuwa sassan Najeriya, wanda yawanci masana'atun yankin ne ke cin gajiyarsa.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Zamfara a shekarun baya ta kasance cibiyar kasuwanci a arewa

Gusau, ta kunshi kabilu da dama da suka hada da Yarabawa da 'yan kabilar Igbo daga kudancin Najeriya da kuma Indiyawa da 'Yan Lebanon. Wannan ne ya haifar da burin yankin na samun jiha, bukatar da ta tabbata a shekarar 1996.

Iyaye a lokacin suna da zabi na makarantun gwamnati masu kyau da kuma makarantun mishan domin ilimin 'ya'yansu.

Ba mu taba tunanin rashin shugabanci nagari ba.

Matsala ce da ta yi tasiri sosai a jihohin arewacin Najeriya, wadanda ke ci gaba da fama da tabarbarewar tattalin arziki, al'amarin da ya yi tasiri ga rayuwar mutanen yankin wadanda yawanci makomarsu ta fi karkata ga kishirwar samun shugabanci nagari.

Wannan matsala ce a bayyane, musamman ta fuskar rashin samar da ayyukan ci gaba daga filin noma da Allah ya albarkaci jihar da arzikin ma'adinan kasa da kuma yawan jama'a.

Sannan babu wani kokari na rage tasirin sauyin yanayi da ake fama da shi. Maimakon tattalin arzikin da Allah ya albarkaci yankin da shi domin taimakawa jama'a tare da ilmantar da 'ya'yansu amma 'yan siyasa sai dai su wadatar da kansu.

Karin bayani game da Zamfara:

  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu

Gwamnatocin da suka mulki kasar a jejjere sun ta yin buris wajen kawo maslaha ta dindindin kan matsolin da ke addabar jihar.

A yayin da matsalar barayin shanu ta zama bala'i ga jihar Zamfara, Gwamna Abdulaziz Yari ya samar da kungiyar 'yan kato da gora don yakar maharan a shekarar 2013.

Sai dai ba a dauki dogon lokaci ba mazauna yankin suka fara korafi kan 'yan kato da gorar, wadanda a yanzu su ma suke gallabar mutanen da ya kamata su kare da sace-sace.

Hakan ta sa kauyukan da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan kato da gora suka fara kokarin ganin sunkare kansu da duk abun da ya kamata.

Daga haka sai rikicin ya kara ruruwa ta hanyar kai hare-hare da daukar fansa. A haka sai a ka kasa cimma kokarin shirin yin afuwa da aka so gabatarwa.

A yanzu dai muna ganin yadda rikici ke kara bazuwa da karuwa kuma ga alama ba a san hanyoyin da za a bi a shawo kansa ba.

Abun da yake a bayyane kawai shi ne yadda dumbin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba ke ci gaba da mutuwa.

Gwamman mutane sun mutu a 'yan watannin da suka gabata sakamakon hare-haren da aka kai wasu kauyuka a jihar Zamfara.

Sai dai saboda rashin isassun maso kawo bayanai, zai yi wahala a fadi adadin mutanen da suka mutu a rikicin da aka shafe shekara shida ana yi.

A ranar 28 ga watan Maris ne wasu mahara a kan babura suka yi wa a kalla mutum 28 yankan rago a kauyen Bawar Daji, mai nisan kilomita 90 daga Gusau.

Wadanda aka kashe din dai suna halartar wata jana'iza ce ta wasu mamatan da aka kashe su ma a irin wannan hari.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Rikicin da ake ta samu ya jawo asarar dumbin rayuka a Zamfara

A tsawon shekarun da suka gabata ana ci gaba da samun matsalolin satar mutane don kudin fansa da kuma fyade a wasu kauyuka na jihar Zamfara.

Ba a ba da rahotan abin sosai saboda ba a cika damuwa da wadanda abun ya shafa a kasa ba: talakawa ne, mutanen kauye, wadanda suka dogara da noma da kiwo kawai a yankunan da ke nesa da inda gwamnati take.

Rikicin ba irin fito-na-fiton da kafofin yada labarai na Najeriya ke sahukin bayar da labarinsa ba ne; tun da ba rikici ba ne a tsakanin Kiristoci da Muslumi, ko tsakanin Arewa da Kudu, ko tsakanin Hausa-Fulani da wasu kabilu.

Ke nan ba labari ba ne da za a iya bayar da shi don kafa hujja game da bambance-bambancen addini da kabilanci da ke tsakanin al'ummar Najeriya ba, saboda al'ada da adinnin maharan da wadanda ake kai wa hari galibi daya ne.

Wannan yana nuna irin gazawar gwamnatin taryya ne wacce ta kasa iya yin abun da ya kamata na kare mutanenta. Don haka an bar mutanen Zamfara da irin kaddarar da ta same su.

A fadin Najeriya akwai manyan wurare da yawa wadanda ake samun rikice-rikice sakamakon rashin matakan tsaro.

Dajin Rugu babban daji ne da ya ratsa yankuna da dama da suka hada da jihar zamfara har kan iyakar Jamhuriyyar Nijar.

Ana ganin dajin tamkar na Sambisa da ke jihar Borno, wanda ya zama maboyar mayakan kungiyar Boko Haram a shekarun baya-bayan nan.

Wani kwararre da ya san yankin sosai Chris Ngwodo, ya ce yanayin da ake fama da shi a jihar Zamfara iri daya ne sak da wanda jihar Borno ta samu kanta a ciki a tsakanin 2009-2010, yayin da kungiyar Boko Haram ta kaddamar da hare-hare masu muni.

"Abun da ke faruwa a Zamfara yanayi ne da zai iya samar da wani rikicin da zai iya ci ya ki cinyewa." in ji Mista Ngwodo.