Me ya sa 'yan Kenya suka biya $10,000 don kallon auren Yarima Harry?

Kenya Royal Wedding

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Baki sun biya shiling miliyan daya daidai da naira miliyan 3.6 don kallon bikin

Wata kafar watsa labarai ta Kenya ta ruwaito cewa baki a wani otel din da ke babban birnin kasar, sun bugi kirji sun biya shillings miliyan daya, daidai da $10,000 ko naira miliyan 3.6, don kallon bikin auren masarautar Birtaniya a kan wani babban majigi.

Rahotanni sun ce an sayar da dukkan tikitin da aka tanada don shiga wajen nuna taron bikin, wanda aka yi a otel din Windsor Golf da Country Club, da ke wajen birnin Nairobi.

An wadata baki da abinci iri-iri, san nan washe-gari kuma suka shiga jirgi mai saukar ungulu zuwa Tsibirin Mount Kenya don yin karin kumallo.

Wasu saurayi da budurwarsa sun ce sun je ne domin samun dabarun da za su yi amfani da su yayin bikin aurensu.

"Za mu yi aure kwanan nan, saboda haka mun zo don samun dabaru na yadda za mu aiwatar da bikinmu. Wannan taron ya kasance mai dadi kuma wanka ya biya kudin sabulu", kamar yadda suka shaida wa Jaridar Standard.

Wannan taron ya jawo suka da ce-ce-ku-ce sosai saboda yadda aka biya irin wannan makudan kuddade kawai don kallon biki a talbijin, a kasar da miliyoyin mutane ke rayuwa cikin talauci.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An sayar da dukkan tikitin da aka tanada don shiga wajen nuna bikin, wanda aka yi a otel din Windsor Golf da Country Club, da ke wajen birnin Nairobi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wata bakuwa ta sanya rigar amare ta kuma shiga wajen da aka nuna bikin tana tikar rawa