Wani mutum ya kira wa alade 'yan sanda a Amurka

alade

Asalin hoton, North Ridgeville Police Department

Bayanan hoto,

Wani dan sanda ya samu ya daure aladen a bayan motar 'yan sandan, kuma har ma ya dauki hoton aladen

'Yan sanda sun saba da samun kira daga wajen jama'a, amma kiran da wani mutum ya yi musu a wata safiyar Asabar a Jihar Ohio ta Amurka, ya sha bamban da sauran.

Jami'ai sun yi tunanin cewa mutumin ba ya cikin hayyacinsa ko mafarki yake ko kuma ya sha giya ya bugu ne a lokacin da ya ce wani alade 'mai naci' na bin sa gida.

"Mun amsa kiran mutumin wanda muka yi tsammanin a buge yake, yayin da yake komawa gidansa daga mashaya da misalin karfe 5.26 na safe," a cewar 'yan sandan kamar yadda suka wallafa a shafinsu na Facebook.

Amma a yayin da suka isa sai suka samu wani mutum da ke cikin hayyacinsa, wanda bai damu da kawo naman alade gida ba.

Rundunar 'yan sanda ta Arewacin Ridgeville, ta ce tabbas aladen ya yi ta bin mutumin, wanda ba a gano ko wanene ba, kuma mutumin ya rasa yadda zai yi da aladen.

Wani dan sanda ya samu ya daure aladen a bayan motar 'yan sandan, kuma har ma ya dauki hoton aladen.

Sai aka kai aladen wani keji da ake ajiye karnukan 'yan sanda - kafin daga bisani a mayar da shi wurin mai gidansa ranar Lahadi da safe.

'Yan sanda sun ce: "Za mu fadi wani abun al'ajabi dangane da aladen da aka sa a motar 'yan sanda, don duk wanda ke ganin kamar almara ce cewa aladen ya nace da bin mutumin to ya sake tunani."