Kun san kasar da aka fi samun saukin yin azumi?

tsawon azumi

A ranar 17 ga watan Mayu ne aka fara azumin watan Ramadan na shekarar 2018 a yawancin sassan duniya.

Musulami suna shafe wata daya suna azumi na kwana 29 ko kuma 30 a watan Ramadan, daga fitowar Alfijir zuwa faduwar rana.

Amma tsawon sa'o'in azumin ya bambanta daga kasa zuwa kasa, yayin da azumin wasu kasashe bai kai na wasu kasashen tsawo ba.

A lokacin zafi, kasashen da ke arewacin duniya kamar na Turai suna shafe yini mai tsawo kafin su yi buda baki, yayin da wasu kasashen Afirka kuma ke fuskantar matsanancin zafi a lokutan bazara.

A wannan shekarar dai azumi a kasashen duniya ya bambanta daga sa'o'i 10 zuwa sa'a 22.

BBC ta yi nazari kan sa'o'in azumi na wasu kasashen duniya.

Jerin wasu kasashe da tsawon sa'o'in da suke azumi

Greenland ita ce kasar da ta fi ko wacce tsawon sa'o'in azumi. Su kan dakata da sahur da karfe 2:00 na tsakar dare, su kuma sha ruwa da misalin karfe 12 na tsakar dare.

Daga cikin kasashen da ke shafe sa'a 20 suna azumi kuma akwai:

Iceland da Rasha wadanda ke daina sahur tun karfe 2 na dare, su kuma sha ruwa da misalin 10 na dare.

Birtaniya na shafe sa'a 19

China da Faransa da Kanada kan shafe sa'a 17 suna azumi

Wasu yankunan Amurka kan shafe sa'a 15, yayin da wasu ke shafe sa'a 17

Afghanistan kan shafe sa'a 16

Saudiyya da Libya da Masar da Pakistan da Indiya da Moroko kan shafe sa'a 15

Kasashen kamar Najeriya da Senegal kan shafe sa'a 14

Kenya da Indonesiya kan shafe sa'a 13

Australiya na da sa'a 11 yayin da Chile kuma ta fi ko ina karancin sa'o'in azumi, inda take da sa'a 10.