Karanta yadda kabilun Najeriya ke buda-baki

Kayan Bude baki

Cikin watan Ramadan Musulmai suna azumi daga fitowar alfijir zuwa faduwar rana inda suke kaurace wa ci da sha.

A lokacin buda baki su kan karya azumin ne da abinci iri-iri kamar yadda al'adun ko wacce kabila yake.

A Najeriya dai Hausawa suka fi yawan Musulmai kuma yawancinsu suna zaune ne a arewacin Najeriya.

Galibin Hausawa musulmai kan buda baki ne da dabino ko kunu da kosai, sai kuma su biyo bayan su da abincin alfarma kamar shinkafa ga masu hali da sauran kayan kwalam, ga marasa hali kuwa su kan ci abun da ya sauwaka ne kawai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Irin wannan kosan da ake tuya a birnin Abidjan dake kasar Ivory Coast na cikin abin da ake ci a lokacin bude baki a kasar. A kasar Hausa ma ana cin kosai lokacin bude baki

Yarbawa ma dai suna buda baki ne da ababen marmari kamar dabino da lemo da sauransu.

Sai dai bayan haka suna shan kunu irin nasu na gargajiya da kuma alale ko kosai, ba ya ga abinci kamar shinkafa.

Image caption Baya ga dabino da sauran kayan marmari Yarbawa dai suna shan kunu da alale ne

Kamar sauran wuraren da al'ummar musulmi kan yi azumin watan Ramadan mai alfarma, su ma al'ummar Igbo musulmi suna da nau'o'in abinci iri-iri da su kan yi buda baki da su.

Alal misali, akwai abinci mai ruwa-ruwa kamar 'pap' (wato koko), da 'akara' (wato kosai), da 'abacha' (wanda akan yi da rogo, a hada shi da ganyen yalon bello da yaji da gishiri da 'okazi' da nama ko kifi ko ganda).

Akwai kuma nau'o'in abinci masu dan nauyi-nauyi irin su 'Okpa' (wanda akan yi kamar alala da gurjiya), da 'akpu' (mai kamar tuwo da akan yi da rogo), wanda akan ci da miya kamar ta ganye ko egusi ko ta kubewa.

Su ma Igbo suna da abinci irin sakwara (wadda akan tuka kamar tuwo da doya), da taiba (wadda ita ma akan tuka kamar tuwo da garin kwaki), kuma dukkansu ana cin su ne da miya kamar ta ganye ko egusi ko ta kubewa.

Wani abin lura a nan kuma, shi ne dukkan wadannan nau'o'in abinci sukan dace da irin abincin da mai azumi ke bukata, don buda baki da sahur.

Saboda suna da sinadarai masu gina jiki, kamar yadda masu ilimin abinci suka nuna.

Image caption Wasu kenan suna bude baki a birnin Maiduguri na jihar Borno

Musulunci na da dadadden tarihi a kasar Kanuri da ya dara shekara dubu daya.

A kasar Kanuri da ke arewa maso gabashin Najeriya ana buda baki da kunun gero da na masara da aka fi sani da mardam da sauran kayayyakin abinci irin su burabisko da sauransu.

Kamar a cikin hotunan da aka wallafa a iya ganin wajen wani bude baki a birnin Maiduguri inda ake shan kunun mardam da kosai da dankalin Hausa da kuma alale.

Sai dai kuma wadannan ba su kadai bane kabilun Najeriya da ke da Musulmai masu azumi cikin watan Ramadan ba. Amma a iya cewa wasu daga cikin sauran kabilun musulmai, kan yi buda bakin ne da irin abincin da Hausawa kan ci.

Labarai masu alaka