Tattalin arzikin Najeriya ya ja baya

Ministar Kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun

Asalin hoton, DEJI YAKE

Bayanan hoto,

Gwamnatin Najeriya na yunkurin rage dogaron da arzikin kasar ke yi da man fetur

Tattalin arzikin Najeriya ya ja baya a rubu'in farko na bana, a cewar wani rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta wallafa a kan yawan arzikin da kasar, wato GDP.

Rahoton na NBS dai ya nuna cewa a rubu'in na farkon 2018 yawan arzikin da Najeriya ta samar ya karu da kashi 1.95 cikin dari idan aka kwatanta da bara warhaka; ya kuma yi kasa da kashi 0.9 cikin dari idan aka kwatanta da rubu'i na hudu na bara.

Wannan ne dai karo na farko da tattalin arzikin kasar ya dan yi kasa tun bayan farfadowar kasar daga koma-bayan da ya afka mata a shekarar 2016.

A cewar hukumar ta NBS, daukacin arzikin Najeriya a rubu'in na farkon 2018 ya kama Naira tiriliyan 28.464, yayin da yawan arzikin idan aka yi la'akari da hauhawar farashin kayayyaki ya tashi Naira tiriliyan 16.106.

Rahoton dai ya kasa arzikin da kasar ke samu gida biyu: da wanda aka samu ta hanyar fitar da danyen man fetur da kuma wanda aka samu ta wadansu hanyoyin.

Shugaba Muhammadu Buhari dai ya kuduri aniyyar yaye kasar daga dogaron da tattalin arzikinta ya yi da man fetur, amma wannan yunkuri na fuskantar kalubale.

A cewar hukumar NBS, a rubu'in na farkon 2018 bangaren man fetur ya bunkasa da kashi 14.77 cikin 100 idan aka kwatanta da rubu'in farkon 2017, yayin da bangaren da ba na man fetur ba ya bunkasa da kashi 0.76 cikin 100 a daidai wannan lokaci idan aka kwatanta da rubu'in farko na 2017.

Harkar noma ce dai kashin bayan ci gaban da ake samu a bangaren da ba na man fetur ba, sai dai ita ma ta fuskanci koma-baya da kashi 1.23 cikin dari idan aka kwatanta da rubu'in karshe na 2017, ko da yake ta bunkasa da kashi 3 cikin 100 idan aka kwatanta da rubu'in farko a 2017.

Ana auna yawan arzikin kasa ne (wato abin da ake kira GDP) ta hanyar yin raskawanar abin da daidaikun mutane suka kashe, da abin da kudin shigar gwamnati, da cinikin da 'yan kasuwa da masana'antu suka yi, da kuma kudin da aka samu ta hanyar fitar da kayayyaki waje.