Barack Obama da matarsa Michele za su fara yin fim

Michelle Obama and Barack Obama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A farkon shekarar 2017 ne ma'auratan suka bar fadar White House

Tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da matarsa Michelle Obama za su hada karfi da karfe da kamfanin Netflix wajen yin fim da kuma shirye-shiryen da za a gabatar a talbijin.

Netflix ya ce tsohon shugaban kasar Amurka da matarsa sun sa hannu kan yarjejeniyar shekara guda da kamfanin.

"Ni da Barack mun yi iitifakin cewa bayar da labari abu ne da ke kara mana kwarin gwiwa," in ji Michelle Obama.

Kawo yanzu babu cikakken bayani a kan yadda za a tsara shirye-shiryen.

Ma'auratan sun bude wani kamfanin yin fim wanda zai tsara shirye-shiryen da za a gabatar a Netflix.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ma'auratan sun ce suna son karfafa gwiwar mutane masu basira wadanda za su iya sa a samu fahimtar juna a tsakanin al'umma

"Daya daga cikin abubuwan da suka rinka faranta mana rai lokacin da muke gwamnati shi ne irin mutanen da muka rika haduwa da su wadanda suka fito daga fannonin rayuwa daban-daban, kuma muna son su bai wa sauran mutane labari kan abubuwan da suka faru a rayuwarsu," in ji Mr Obama.

"Shi yasa ni da Michelle muka ga cewa zai yi kyau idan muka kulla kawance da Netflix, - muna son mu raya mutane masu basira tare da karfafa musu gwiwa wadanda za su iya sa a samu fahimtar juna a tsakanin al'umma, kuma mu taimaka mu su a kan yadda za su bai wa duniya labarin rayuwarsu."

Mrs Obama ta ce: "Ni da Barack mun yi amanna cewar ba da labari abu ne da ke tasiri kuma yana karfafa mana gwiwa, kuma yana sa mu sake tunani akan abubuwan da ke faruwa a duniya, sannan yana taimaka mana sanin yadda za mu karbi kowa da kowa."

Ta kara da cewa: "Kuma kamfanin Netflix shi ne kafar da ya dace mu yi amfani da shi saboda akwai abubuwa da mu ke son mu bayar da labarinsu, kuma mun zaku mu ga ranar da hadin gwiwar zai fara aiki."