Halin da na ga 'yan gudun hijira ya sa ni zubar da hawaye — Priyanka

Priyanka Chopra

Asalin hoton, Vulture

Bayanan hoto,

Priyanka Chopra

Priyanka Chopra, ba wai kawai jaruma ce da take fitowa a fina-finai ba, tana matukar bayar ga gudunmuwa ga al'umma har ma da kyautata walwalar wasu mutane mabukata musamman yara.

Kazalika Priyanka ta kasance jakadiyar sadar da zumunci da kuma kare hakkokin yara a Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unicef.

Irin halayyar Priyanka na bayar da gudunmuwa ga al'umma, ya sa ta ziyarci sansanin 'yan gudun hijra mafi girma a Bangladesh tare da abokan aikinta na kungiyar..

Priyanka ta wallafa hotuna da kuma bayanai a kan ziyarar ta ta a shafukanta na Twitter da kuma Instagram.

Asalin hoton, India Today

Daga cikin bayanan da ta wallafa ta ce " Yara suna barin matsugunnansu, yakamata a kula da irin wadannan yara domin suna matukar bukatar kulawa".

Priyanka, ta ce halin da ta ga yara a sansanin 'yan gudun hijrar da suka kai ziyarar, ya sa ta zubar da hawaye saboda tsabar tausayi.

Fiye da shekara 10, Priyanka na aiki tare da Unicef a matsayin jakadiya.

Jarumar tana kuma kokari ta daukaka muhimmancin muhalli da lafiya da ilimi da kuma 'yancin mata.

Priyanka, a cikin sakonnin da ta wallafa a shafinta na Instagram, ta ce ziyarar da ta kai daya daga cikin sansanin 'yan gudun hijra mafi girma a duniya, babban tarihin ne, domin ta samu darussa da dama a ziyarar.

Asalin hoton, Daily Bangladesh

Sun dai kai wannan ziyara ce domin gani da kuma tallafawa 'yan gudun hijrar da ke zaune a sansanin, musamman mata da kananan yara.

Rikicin jihar Rakhine ta kasar Myanmar ne ya tursasawa musulmi 'yan kabilar Rohingya su kusan dubu 700 tsallakawa makwanciyar kasarsu wato Bangladesh domin neman tsira, kuma kaso 60 cikin 100 na wadannan mutane, yara ne.

Priyanka Chopra ta nuna matukar tausayi da yadda ta ga ana rayuwa a sansanin, hakan ya sa ta ce yakamata kasashen duniya su rinka tallafawa irin wadannan mutane da suka tsinci kan su cikin zama a sansanin 'yan gudun hijra.

Jarumar ta dauki hotuna tare da mutanen da ke zaune a sansanin, musamman ma yara, ta rike hannusu ta dauki wasu daga cikin kananan yaran a hannunta tana kuma dariya.

Asalin hoton, Daily Sun