Za a fara amfani da Faransanci a Ghana

Kasashe masu makwaftaka da Ghana suna amfani ne da harshen Faransanci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kasashe masu makwaftaka da Ghana suna amfani ne da harshen Faransanci

Ghana za ta fara amfani da yaren Faransanci a matsayin yare na biyu a hukumance, bayan turancin Ingilishi.

Dama akwai yarjejeniyar tsakanin kasar ta Ghana da kungiyar kasa da kasa ta masu amfani da yaren Faransanci domin bayar da tallafi na taimakawa ta yadda za a inganta hanyar koyo da koyar da faransanci a kasar.

Wani tsohon ma'aikacin hukumar ilimi ta Ghana, Sheikh Armiya`u Shu`aib, ya ce akwai alamun cewa Ghana ta dauki wannan mataki ne domin zai iya taimakawa ta fannin tsaron kasa da kasuwanci.

Sannan zai kara dankon zumunci tsakanin Ghana da kasashe masu amfani da yaren Faransanci da ke makwaftaka da Ghana, In ji Sheikh Armiya'u.

A baya dai akwai makarantu kalilan da suke koyar da yaren Faransanci a kasar ga wadanda ke so su koya.

A makarantu kuwa dalibai na da zabi na harshen da za su koya, tsakanin daya daga cikin harsunan cikin gida ko kuma Faransanci.

A cewar tsohon jami'in, a yanzu zai zama wajibi ga mutane su koyi harshen na faransanci kasancewar ya zama na biyu a cikin harsunan da za a rinka amfani da su a kasar a hukumance, baya ga turancin Ingilishi.