'An yi safarar dalibai a kalla 100 daga Najeriya zuwa Turai'

dalibai

Asalin hoton, Gwamnatin jihar Edo

Bayanan hoto,

Solomon Okoduwa na rangadin makarantu da ke jihar Edo inda yake mu su magana akan hadarin da ke cikin safarar mutane.

Malaman wata makaranta da ke kudu maso kudancin Najeriya sun bayyana cewa dalibai a kalla 100 ne suka bata a cikin watani hudu da suka wuce, kuma ana kyautata zaton cewa masu safarar mutane ne suka fitar da su daga kasar.

Malaman makarantar ne suka fadawa babban mataimakin gwamnan jahar na musamman a kan safarar mutane da masu yin kaura ta haramtaciyyar hanya Solomon Okoduwa, lokacin da ya kai ziyara makarantar, wadda ke birnin Benin na jihar Edo.

Mr Okoduwa ya shaida wa sashen Pidgin na BBC cewa, da farko malaman sun dauka cewa daliban da suka bata, sun kamu ne da rashin lafiya.

Amma daga baya, an gano daga sauran dalibain cewa an wuce da su ne zuwa Libya, inda daga nan watakila su yi kokarin tsallaka wa mai cike hadari zuwa Turai.

Ba a san mai yasa suka tafi ba, ko kuma idan wani ne ya tunzura su ba.

"Lokacin da muka tambayi malaman a kan yadda suka tattara bayyanan, sai suka fada mana cewa sun ji labarin ne daga bakin sauran dalibai cewa sun yi tafiya," in ji shi.

Mr Okoduwa ya kara da cewa za su cigaba da gudanar da taruruka na wayar da kai a makaratun da ke Jihar Edo domin kowa ya samu damar bayyana ra'ayinsa.