Lemar kwadi ta kashe mutum 11 ta kwantar da mutum 800 a Iran

Wata lemar kwadi mai guba da aka dauki hotonta a Berlin, na kasar Jamus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ba a dai san irin nau'in lemar kwadin da suka ci ba amma akwai wata mai guba da ake kira Amanita phalloides, ko death cap da Turanci, da ake samu a Iran

Fiye da mutum 800 ne suka fara rashin lafiya bayan da suka ci lemar kwadi mai guba a larduna 10 da ke yammacin Iran.

Mutum a kalla 11 ne suka mutu yayin da aka kwantar da daruruwa a asibiti.

Babu magani mai tasiri da za a bai wa wadanda suke fama da wannan lalura, a cewar kamfanin dillancin labarai na Tasnim.

A kalla mutum biyu ne aka yi wa dashen hanta. Lemar kwadin ta yi kama da irin wadda aka saba ci.

An yi kira ga mutane a kan ka da su saya da lemar kwadin da ta saki, kuma su tabbatar da cewa lemar kwadin da ke cikin ledar da aka rufe bakinta kawai za su saya a shaguna.

A cewar sashin Fasha na BBC, a wasu lokutan ana sayar da lemar kwadi kan titunan Iran kuma babu tabbas game da shawarar da mutane kan bayar da a kan wadda za a iya ci.

Shukar na tsirowa ne a yankin yammacin Iran mai tsaunuka, a cewar Tasnim.

Bakwai daga cikin wadanda suka mutu sun fito ne daga yankin Kermanshah.

Rahotanni sun ce ruwan sama da ke yi a kwanakin baya-baya nan ya sa an samu karuwa a yawan lemar kwadin da ke tsirowa.

Image caption Taswirar Iran

Labarai masu alaka

Karin bayani