Kiristoci suna zanga-zanga kan kashe 'yanuwansu a Najeriya

Catholics dey match for street
Bayanan hoto,

'Yan darikar Katolika da ke Lagos sun gabatar da addu'o'i kafin su fita zanga-zangar zuwa wajen sakatariyar jiha a Alausa

Kiristoci 'yan darikar katolika sun taru a sassa daban-daban na Najeriya don yin zanga-zangar lumana a ranar talata, don nuna adawa da 'yawan kashe' musu mutane da sauran 'yan kasa da suka ce ana yi.

Zanga-zangar tasu na zuwa ne a yayin da suke jana'izar wasu manyan shugabannin darikar biyu da ake zargin makiyaya ne suka yi a Cocin St. Ignatius Catholic Parish, da ke Ayar Mbalom a karamar hukumar Gwer Ta Gabas, kimanin wata guda da ya gabata.

Shugaba Buhari dai ya aike da sakon jaje a lokacin da aka kai wannan hari, ya kuma sha alwashin zakulo maharan da kuma hukunta su.

Kungiyar Bishof-Bishof ta Najeriya ta bai wa dukkan 'yan darikar Katolika da ke fadin kasar umarnin fitowa su yi zanga-zangar lumana da kuma gabatar da addu'o'i, wadda suka kira 'March for Life,' a ranar Talata, don su nuna wa gwamnati fushinsu kan abun da ke faruwa.

Bayanan hoto,

Kungiyar Bishof-Bishof ta Najeriya ta bai wa dukkan 'yan darikar Katolika da ke fadin kasar umarnin fitowa su yi zanga-zangar lumana da kuma gabatar da addu'o'i

Tuni dai gwamnan jihar Benue Samuel Ortom ya ayyana ranar Talata a matsayin ranar hutun aiki don girmama wadanda suka mutun.

Wakiliyar BBC da ta halarci wajen zanga-zangar a Abuja ta ce mutanen ba su damu da ruwan saman da aka sheka ba da safe, don dumbin mutane ne suka taru.

Wasu daga cikinsu sun yi ta zuwa babban cocin kasa da ke birnin tarayyar don yin addu'a ga mamatan kafin daga bisani su kwarara kan tituna don yin zanga-zangar.

Haka ma wakiliyar BBC da ke birnin Fatakwal ta bi masu zanga-zangar, inda ta ce sun fito da dama don nuna goyon bayansu kan abun da darikar katolikan ta umarta da su yi.

Babban Bishop din katolika na Fatkwal din Camilus Etokudoh, ya tunasar da kowa cewa rai abu ne mai matukar muhimmanci, ya kuma yi Allah-wadai da kashe mutane da ake yi.

Ya kuma kara da cewa zanga-zangar lumanar ba ta da hadi da siyasa don ba zai yiwu a dinga wasa da rayukan jama'a wajen sanya siyasa ba.

"Makiyaya sun kwace mana yawancin filayenmu a kasar nan, kuma za mu ci gaba da aike wa Shugaba Buhari korafi ya zo ya sa baki a cikin batun nan," in ji shi.

Bayanan hoto,

An yi zanga-zangar a wasu manyan biranen kasar

Kazalika shi ma babban Archbishop na darikar Katolika da ke Lagos Rev. Alfred Adewale Martins, kira ya yi ga gwamnati da ta sanya baki da gaggawa cikin lamarin kafin ya zama wani rikicin kabilanci daban.