An sace iyalan wani kwamishina a Zamfara

zamfara map

Wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun sace iyalan wani kwamishina a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da cewa a ranar Litinin da daddare ne aka sace iyalan Alhaji Abdullahi Gurbinbore, wanda shi ne kwamishinan wasanni na jihar, daga gidansa da ke kauyen Gurbinbore, da ke kan iyakar Zamfara da jihar Katsina.

Iyalan kwamishinan da aka sace sun hada da matarsa da 'ya'yansa biyu kanana da kuma wasu mutum biyun daban.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ya ce tuni an kaddamar da bincike na musamman don kubutar da mutanen.

Sace-sacen mutane dai za a iya cewa ya zama ruwan dare a jihohin arewacin Najeriya.

Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron karin bayanin da kakakin rundunar 'yan sanda jihar ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:

Bayanan sauti

Bayanin kakakin 'yan sanda kan sace iyalan kwamishina

Karin bayani game da Zamfara:

  • Karin bayani game da Zamfara:
  • Kashi 67.5 ke rayuwa cikin talauci
  • Iya karatu da rubutu: Kashi 54.7
  • Take: Noma tushen arzikinmu
  • Yawancin mutanen jihar manoma ne daga Hausa Fulani
  • Yawan jama'a: Miliyan hudu da rabi (Alkalumman shekarar 2016)
  • Musulmi ne mafi yawa
  • Jihar da aka fara kaddamar da Shari'a - a 2000
  • Madogara: Shafin alkalumma na Najeriya da wasu