Yadda takari suka yi bikin Larabawa a Najeriya

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Mutanen da suka taba zama a kasar Saudiyya da ake fi sani da Takari sun gudanar da wani biki domin tuna al'adun kasar ta Saudiya da sada zumunta.

Wadanda suka shirya bikin na "Muzmar' a birnin Kano, sun ce ya kuma hada fuskokin mutanen da rabonsu da ganin juna tun a kasar Saudiyya.

Bidiyo: Ibrahim Isa/Yusuf Yakasai