Bidiyon zanga-zangar Kiristoci a Abuja

Daruruwan mabiya addanin kiristan 'yan darikar Katolikane, suka yi tattaki a titunan birnin Abuja, bayan da suka yi addu'o'i a cikin babbar majami'a ta kasa.

Sun nuna rashin jin dadi game da kashe-kashen da ake yi a jihohi da dama na Najeriya.

Masu macin, maza da mata sanye da tufafi masu launuka iri-iri, na dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen neman a kawo karshen kashe-kashen jama'a da ake yi.